Kungiyar EU ta gargadi Iran kan yarjejeniyar nukiliya
May 9, 2019Talla
Kasashen Turai kawayen Iran da kungiyar EU sun jaddada aniyarsu ta cigaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran a shekarar 2015. Sai dai a cewar Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, akwai bukatar a tinkari matsalar cikin hikima. "Ba ma fatan samun karin sabani, muna bukatar amfani da matakan diplomasiyya. Mun san iyakarmu, da zarar Turai ta cigaba da dunkulewa wuri guda. Kuma wannan shi ne matsayarmu. Samun kyakkyawar dama shi ne zai bamu ikon warware matsalar cikin sulhu."
Da ya ke ganawa da manema labaru a fadar White House na Amirka, Shugaba Donad Trump ya ce kofa a bude take ya tattauna kan rikicin kasuwanci tsakaninsa da Iran. Amma ya ce sai sun nuna bukatar haka da kansu.