Kungiyar EU ta nuna fargabar kazancewar rikicin Gabas ta Tsakiya
July 14, 2006Talla
A halin da ake ciki KTT ta nuna fargabar cewa hare haren da Isra´ila ke kaiwa Lebanon ka iya janyo kasar Syria cikin mummunan fadan da ake yi. Ministan harkokin wajen Finland, kasar da ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar EU, Erkki Toumioja ya ce idan haka ya faru to ba wanda ya san karshen rikicin. A lokaci daya ministan ya sanar da cewa a gobe asabar babban jami´in harkokin ketare na EU Javier Solana zai fara rangadin yankin GTT a wani yunkuri na yin sulhu. Shi kuwa shugaban Iran Mahmud Ahmedi Nijad ya yiwa Isra´ila kashedi ne da kada ta kuskura ta kaiwa Syria hari. Yace yin haka tamkar kaddamar da yaki ne akan dukkan kasashen musulmi.