EU: Yarjejeniyar kasuwanci
December 30, 2020Talla
Nan gaba kadan ne a yau Laraba, kungiyar tarayyar Turai ta EU za ta ratabbawa wata yarjejeniyar kasuwanci hannu mai matukar muhimmanci, tsakaninta da kasar Sin ko China. Kimanin shekaru sama da bakwai ke nan aka shafe ana zaman dakon wannan rana da za a shiga wannan yarjejeniyar ta kasuwanci da za ta bunkasa harkokin kasuwancin kasashe mambobin kungiyar Tarayar Turai. Yarjejeniyar dai za ta kunshi samar da daidaiton saka hannun jari tsakanin kamfanonin kasashen na tarayar Turai da China a kasuwannin kasar ta Sin.