1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutukar ganin an ceto Leah daga Boko Haram

September 19, 2018

Masu fafutukar kare 'yan mata 'yan makaranta na Chibok dai sun sake hawa tituna a birnin na Abuja da nufin kara matsin lamba ga gwamnatin na ceto daukacin kammamun.

https://p.dw.com/p/35AtV
Nigeria Demonstration Bring Back Our Girls in Chibok
Hoto: Reuters/A. Akinleye

Kisan na Saifura Ahmad da kuma wa'adin wata guda a kan Leah Sharibu dai daga dukkan alamu na shirin sake tada tsohon miki a bangaren 'yan fafutukar Bring Back Our Girls Movement.

Kuma basu yi wata wata ba wajen sake hawa a tituna na Abuja da nufin kara matsin lamba ga kokari na ceto yan matan na Chibok dari da doriya da ragowar ma'aikatan jinkan Rann dama Leah Shribu dake zaman yar makarantar Dapchi dake a hannu na kungiyar har yazuwa yanzu.

Zanga zangar dai na zuwa ne dai dai lokacin da siyasa ke kara shiga a cikin rudu. Tuni dai manya cikin jiga jigai na kungiyar suka raba gari da Abujar da ma bukatar nema na takara ta shugaban kasar a cikin wasu jam'iyyun adawa

A cikin wannan mako ne dai kungiyar ta Boko Haram ta harbe Saifura Ahmad da ke zaman wata ma'aikaciyar Red Cross da sukai nasarar sacewa a cikin watan Maris din data shude tare da kuma barazanar hallaka ita kan ta Leah Sharibu din in har mahukuntan na Abuja basu sassanta ba ya zuwa karshen watan.