1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar gamayyar turai ta bawa Congo karin talafin euro million 165

Zainab A MohammedSeptember 4, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5c

Hukumar gudanarwa ta kungiyar gamayyar Turai EU,ta sanar da bada karin tallafin euro million 16,kwatankwacin dala million 20.5,wa janhuriyar democradiyyar Congo ,domin gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa.Hukumar gudanarwar,tace wadannan kudade na matsayin martani ne adangane da kira da sakatare general Kofi Annan yayi na bukatar tallafawa kasar.Jamiai sun sanar dacewa,kungiyar ta gamayyar turai kawo yanzu,ta tallafawa Congon da kimanin euro million 165,wanda ke zama kudi mafi tsoka da kasar tasamu na gudanar da zabenta.Bugu da kari kungiyar ta gamayyar turai nada jamianta dake lura da harkokin zaben na congo,baya ga dakarunta dubu 2 dake kula da harkokin tsaro.Kewayen farko na zaben daya gudana ranar 30 ga watan yulin daya gabata dai, ya samu fitowan alummar wannan kasa ,sai sakamakon zaben da aka gabatar a watan augustan daya gabata ya haifar da rikici tsakanin abokan adawa.A ranar 29 ga watan oktoba ne zaa gudanar zaghaye na biyun zaben shugaban kasa,tsakanin shugaba joseph kabila da mataimakinsa Jean-Pierre Benba.