1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Kungiyar IS ta dauki alhakin hari a Iran

Abdullahi Tanko Bala
January 4, 2024

Mutane fiye da 80 suka rasu a tagwayen hare haren IS a Iran wajen juyayin mutuwar Qasem Soleimani

https://p.dw.com/p/4as8J
Harin Bama bamai a Kerman na kasar Iran
Harin Bama bamai a Kerman na kasar IranHoto: MEHR/AFP

Kungiyar IS ta yi ikrarin cewa ita ce ta kai harin tagwayen bama bamai da ya hallaka mutane 84 yayin da ake juyayin zagayowar ranar da aka kashe kwamadan dakarun juyin juya halin Iran Qasem Soleimani wanda Amurka ta hallaka a Iraqi a 2020

Kungiyar ta IS ta wallafa ikrarin a cikin wata sanarwa a shafinta na Telegram.

Tagwayen bama baman sun fashe ne a birnin Kerman a jiya laraba suka kuma hallaka mutane da dama cikin dandazon jama'ar da suka halarci taron alhinin mutuwar Soleimani.

Harin shi ne mafi muni da aka kai cikin Iran a tsawon shekaru 45 a tarihin kasar ta Jamhuriyar Islama.