Kungiyar NATO na taron kolinta
July 11, 2023Ana dai ganin batun kasancewar kasashen Sweden da kuma Ukraine zama mambobin kungiyar ya mamaye zauren taron. Kasar Turkiyya dai ta amince ta gabatar da kudurin shigar kasar Sweden cikin kungiyar gaban majalisar dokokinta nan bada jimawa, adawar Turkiyyar da ke zamewa Sweden din shamaki ga zama mamba a NATO.
Ko da yake dai Turkiyyar bata bayyana takaimaman ranar da za ta gabatar ba. Taron da zai gudana a kusa da Belarus da ke dasawa da Rasha, zai tura mahimmin sako ga gwamnatin Moscow kan mamayar da ta kaddamar kan makwabciyarta Ukraine.
Ana san ran shugabbanin na NATO su amince da tsare-tsare kan yadda za a mayarwa Rasha da martanin hare-harenta, kana su cimma matsaya ta karshe kan tsarin tallafawa Ukraine domin kare kanta daga hare-hare a nan gaba tare da inganta dakarunta. A taron kungiyar da shugabanta Jens Stoltenberg zai jagoranta, wasu kasashen za su bada karin tallafin makamai ga gwamnatin Kyiv.