Kungiyar NATO ta amince da shiga kawacen da ke yakar IS
May 24, 2017Talla
Wata majiyar Diflomasiyya ce dai ta sanar da wannan labari a wannan Laraba. Kasar Amirka dai da ke jagorantar rundunar kawancen da ke yakar 'yan jihadin na ISa kasashen na Iraki da Siriya, ta jima ta na neman shigar kungiyar ta NATO cikin wannan sahu. Wannan batu da jakadun kasashen 28 membobin kungiyar suka aminta da shi, zai kuma samu amincewar shugabannin kasashen kungiyar da za su yi taronsu a ranar Alhamis a birnin Brussels na kasar Beljiyam a cewar majiyar.
Harin da aka kai na birnin manchester ne dai ya kara sanya daukan wannan mataki, inda kawo yanzu hukumomin kasar Libiya suka tabbatar da kama Ramadan Abedi, mahaifin yaron da ake zargi da kai harin na Manchester, bayan da a ranar Talata aka kama yayan shi mai suna Hachem.