1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta gargadi Kungiyar Taliban

Ramatu Garba Baba
August 10, 2021

Kungiyar Tsaro ta NATO ta gargadi mayakan Taliban kan kaucewa yunkurin kwace mulki da karfin tuwo inda ta nemi kungiyar da ta gaggauta tsagaita bude wuta.

https://p.dw.com/p/3ymCs
Brüssel NATO Gipfeltreffen
Hoto: Brendan Smialowski/AFP/AP/picture alliance

Kungiyar tsaro ta NATO, ta yi kira ga Kungiyar Taliban da ta gaggauta tsagaita bude wuta a fadan da ta ke da gwamnatin kasar Afghanistan. Nato ta ce kasar na cikin matsanancin yanayi mai tattare da hadura da kuma manyan kalubale, a halin da ake ciki, ta ce karfin soji ba zai kawo mafita daga rikicin ba.

A jawabin Kungiyar, wani babban jami'inta, ya ja kunnen Taliban a game da yunkurin son karbe iko da karfin tuwo, ya ce, ba za a taba amincewa da duk wata gwamnati da za ta kafa ba koda ta sami nasara a yakin da ta ke.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a na shi bangaren, ya ce, Taliban ta aikata laifuka na kisan fararen hulan da wasu na'ukan cin zarafin bil'adama a yayin wannan rikicin..

Daruruwa sun rasa rayukansu a yayin da dubbai ke ci gaba da tserewa daga kasar tun bayan da mayakan Taliban suka kaddamar da hare-hare da karbe iko na manyan biranen kasar.