Mutane sun rasa rayukan su a Afghanistan
July 2, 2018Wani dan kunar bakin wake ya kai hari a tsakiyar babbar kasuwar Jalalabad wacce ke daura da harabar ofishin gwamna a yayin da suke tsaka da ganawa da shugaba Ashraf Ghani.
17 daga cikin mutanen da suka rasa ransu mabiya addinin Sikh da Hindu ne, sai kuma wadansu mutane 20 suka samu raunuka kuma da yanzu haka ke kwance cikin mawuyacin hali a asibiti kamar yadda daraktan lafiyar lardin Najibullah Kamawal ya sanar.
Wata sanarwa da ke fitowa daga ofishin jakadancin kasar Indiya, ta bayyana Avtar Singh Khalsa, dan takara daya tilo mai bin addinin na Sikh a zaben 'yan majalisar dokokin kasar ta Afghnistan da za a gudanar a watan Oktobar a wannan shekara, na daya daga cikin wadanda suka rasa ransu sakamakon wannan hari.
Harin na zuwa ne bayan shugaban kasar ya ba wa jami'an tsaro umarnin cigaba da yaki da 'yan Taliban, bayan karewar wa'adin tsagaita bude wuta a tsakaninsu da gwamnati.