1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO na son taimakawa 'yan Afganistan

Binta Aliyu Zurmi
August 31, 2021

Shugaban kungiyar kawancen tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce ba za su manta da al'ummar kasar Afghanistan ba, kuma ba za su yi kasa a gwiwa wajen ci gaba da yaki da ayyukan ta'addanci ba.

https://p.dw.com/p/3zkSx
NATO Secretary General Jens Stoltenberg
Hoto: Francisco Seco/Pool/AP/picture alliance

Stoltenberg ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a wannan rana ta Talata.

Wannan dai na zuwa ne sa'o'i bayan da Amirka ta kammala ficewa daga Afghanistan, wanda ya sa al'umma a kasashen duniya aza ayar tambaya game da makomar 'yan kasar da ke kokarin ficewa daga kasar amma 'yan Taliban sun hana su.

Koda yake Stoltenberg ya bukaci Taliban da su bude filayen jiragen saman kasar, domin bayar da dama ci gaba da mu'amala da kasashen ketare da kuma bai wa al'ummar ta Afghanistan da suka yi aiki na tsawon lokaci da dakarun kasashen waje damar ficewa ga wadanda ke da muradin yin hakan. 

Ita ma a nata bangaren shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nuna wannan bukatar, inda ta ce idan har ba su bude filayen jiragen saman ba, hatta kayayakin agaji ba za a samu damar kai su ga mabukata ba.