Rasha ta kame wasu jiragen ruwan kasar Ukraine
November 26, 2018Ma'aikatar tsaron kasar Ukraine ta bayyana cewar wasu daga cikin jami'an tsaron kasar da ke cikin jiragen ruwan sun samu munanan raunuka sakamakon wannan hari. A baya gwamnatin Ukraine ta zargi Rasha da kai wa wani jirgin ruwan ta hari a yankin Azov,da take maida martani ma'aikatar tsaron kasar Rasha, ta bayyana cewar tana da hujjoji game da yadda Ukraine ta ke amfani da jiragen yakin ta na ruwa, don neman kulla sabon rikici tsakanin kasashen biyu, wannan dalili ne ya sanya ta kame jiragen ruwa har guda uku na Ukraine .
Tuni dai kakakin kungiyar tsaro ta NATO ta yi kira ga kasar ta Rasha kan ta mutunta dokar walwalar jiragen ruwan Ukraine. A yau ne dai ake saran za'a yi zaman gaggawa na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya kan wannan tashin hankali da ya barke tsakanin kasashen biyu.