Bukatar kawo karshen luguden wuta a Gaza
October 29, 2023Kiran na Josep Borrel ya gamu da shan suka daga bangaren wasu shugabannin kungiyar, inda Firaministan kasar Austria ya ce matakin neman a tsagaita wuta ya saba wa matsayar da EU ta cimma a ranar Asabar.
Karin bayani :EU na nuna damuwa kan halin da 'yan Gaza ke ciki
A nata bangaren kungiyar Red Cross da ke bayar da agajin gagawa ita ma ta yi kira da a gagauta kawo karshen wannan yakin a wani mataki na kauce wa mumunan bala'i da ka iya biyo baya, a daidai lokacin da Isra'ila ta kara tsananta kai hare-harenta.
Red Cross ta bakin shugabanta ta ce dole duniya ta nuna kyama a kan abin da ke faruwa, ta kara da cewa yanzu haka a Zirin Gaza akwai mutane sama da miliyan biyu da ba su da wurin tserewa, kuma ana ci gaba da yi musu luguden wuta.
Ita ma hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da 'yan gudun hijira a yankin Zirin Gaza UNRWA ta bayyan halin ha'ula'in da al'ummar Gaza ke ciki na rashin wutar lantarki da abinci da ruwan sha, ta ce wannan matakin ya saba wa dokokin agaji na kasa da kasa.