Kurdawa za su ajiye makamai a Siriya
September 12, 2016Alamu na nuna cewar 'yan tawayen Kurdawa na YPG a Siriya sun amince da mutunta tayin yarjejeniyar tsagaita wuta da kasahen Amirka da Rasha suka cimma a ranar Lahadi. To sai dai a safiyar Litinin, kungiyoyin sa ido sun bada rahotannin barin wuta da bama-bamai tsakanin bangarorin gwamnati da na 'yan awaren gwamnati a birnin Aleppo.
A nata bangaren gwamnatin Turkiya ta kuduri aniyar tura kayan agajin gaggawa da suka hada da kayan abinci da tufafi da zarar yarjejeniyar tsagaita wutar ta yi tasiri sannan akwai kyakkyawan fatan dakarunta za su kakkabe mayakan IS da ke samun mafaka a yankin ta.
To sai dai Shugaban Siriya Bashar al-Assad ya sha alwashin gwamnatinsa za ta samu galaba a kan dukkanin 'yan tawaye da ke barazana ga gwamnatin sa. Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Birtaniya ta bayyana goyon bayan ta ga cimma nasarar tsagaita wuta tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye a Siriya.