Gwamnatin Siriya ta yi watsi da yunkurin Kurdawa
March 16, 2016Babban jakadan kasar Siriyan a Majalisar Dinkin Duniya Bashar Ja'afari ne ya bayyana hakan a yayin taron sulhunta rikicin kasar da ke ci gaba da gudana a birnin Geneva na kasar Switzerland, inda ya ce da amincewarsu ne ma kasar Rasha ta fara janye dakarunta daga kasar.
"Matakin fara janye dakaru daga kasar Siriya da mahukuntan Rasha suka dauka sun yi shi ne bisa yarjejeniyar da muka cimma a tsakaninmu. Shugabannin kasashen biyu Vladmir Putin na Rasha da takwaransa na Siriya Bashar al-Assad sun cimma yarjejeniya. Kafin Rasha ta turo dakarunta Siriya sai da muka amince, kana in za ta janye wasu ko baki dayan sojojinta daga kasar ko ma sauya akalar yakin sai duka bangarorin biyu sun amince."
Matakin fara janye dakarun kasar ta Rasha daga Siriya dai ya samu karbuwa daga al'ummomin kasa da kasa har ma da kungiyar tsaro ta NATO.