Kuri'ar kin amanna da Gerhard Schröder
July 1, 2005Shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya cimma bukatarsa a game da gudanar da sabon zabe na gaba da wa’adi ko da yake a yanzun shawara ta rage hannun shugaban kasa Horst Köhler a game da rushe majalisar dokokin dake ci a yanzun. Shugaban na da sararawa ta tsawon makonni uku domin tsayar da shawara, saboda a hakikanin gaskiya gwamnatin hadin guiwa ta SPD da the Greens na da cikakken iko da kuma amanna domin ci gaba da tafiyar da al’amuran mulki har ya zuwa ranar da za a tsayar domin gudanar da zaben. Ainifin kuri’ar kin amanna da salon kamun ludayin shugaban gwamnatin da wakilan SPD da the Greens suka yi, ba kome ba ne illa nuna biyayya ga Gerhard Schröder dangane da wannan bukata tasa. A karkashin wani hukunci na kotun koli ta Jamus, irin wannan manufa ta kin amanna da salon kamun ludayin shugaban gwamnati ta halasta idan dukkan jam’iyyun siyasar dake da fada a ji suka bayyana bukatar gudanar da wani sabon zabe na gaba da wa’adi, sannan ita kuma gwamnati ta tabbatar da cewar bata da cikakken ikon magance matsalolin dake addabar kasa baki daya. A sabili da haka ne Gerhard Schröder bai yi wata rufa-rufa ba wajen yin nuni da irin matsalolin da yake fama da su daga su kansu wakilan SPD a majalisar dokoki. Wannan maganar ta shafi manufofinsa na garambawul ga kasuwar kodago da kuma yunkurinsa na kawo canji ga tsarin jin dadin rayuwar jama’a. Kazalika a maganar dangantakar Jamus da kasashen Rasha da China. Sannan matsala ta biyu ta danganci rinjayen da ‚yan christian Democrats suke da shi ne a majalisar gwamnonin jiha. Saboda wannan majalisa ta kann taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da wasu kudurorin da suka shafi makomar tarayya baki daya. Wannan majalisa tana iya hana ruwa gudu wajen wanzar da wasu kudurori. Matsalar ta kara yin tsamari tun bayan da ‚yan Christian Union ke da rinjaye a kwamitocin bincike da majalisar dokoki ta Bundestag da ta jihohi ta Bundesrat ke nadawa. Yawa-yawanci zaka tarar da sabanin da ake fuskanta bai shafi ainifin maganar dake akwai ba, duka-duka lamarin ya danganci bukatun jam’iyyun ne a wawware ta yadda ake shan fama da wahala a kokarin cimma wata manufa mai sassauci a tsakani. Babban abin da shugaban kasa Horst Köhler zai mayar da hankali kansa a yanzun shi ne ya tantance ainifin adawar da shugaban gwamnati Gerhard Schröder ke fuskanta daga wakilan gwamnatinsa ta hadin guiwa dangane da manufofinsa na garambawul. Idan har zarafi ya kama aka tsayar da shawarar gudanar da sabon zabe na gaba da wa’adi to kuwa ba shakka za a fuskanci yakin neman zabe mai tsananin gaske, kamar yadda aka fara hange tun a yanzun.