Shugaban gwamnatin Ostiriya zai sauka
October 10, 2021A farkon makon nan, masu shigar da kara na Ostiriya sun ce ana binciken shugaban gwamnati da wasu mutane tara da laifin cin hanci bayan masu bincike sun kai samame a ofisoshin jam'iyya mai mulki.
Kodayake jam'iyyar ÖVP ta yi watsi da zargin da jam'iyyar The Greens ta yi wa Shugaba Kurz, inda nemi da ya yi murabus a ranar Juma'a.
Mataimakin shugaban gwamnatin kuma jagoran jam'iyxyar the Greens, Werner Kogler ya ce Kurz "bai dace da mukami ba" kuma yayi kira ga jam'iyyar ÖVP da ta zabi mutumin da ba a iya kushewa don maye gurbinsa.
Sai dai Kurz ya ce yana so ya ci gaba da shugbantar ja'iyyarsu ta Austrian People's Party (ÖVP), tare da komawa majalisa a matsayin shugaban rukunin jam'iyyar. Tsohon ministan harkokin waje na kasar Alexander Schallenberg shi ne zai zama sabon shugaban gwamnatin tarayya idan Sabatine Kurz ya sauka.