Kwallon kafa: Gasar zakarun nahiyoyi
kasashe takwas da suka halarci gasar zakarun nahiyoyin da su ne: Portugal da Chile da Kamaru da Mexico da Australia da New Zealand da mai masaukin baki Rasha sai kuma Jamus da ke rike da kambu. Kwanaki 15 ne za su yi.
Baki da masu masaukin baki
Rasha dai ba ta yi rawar gani ba a gasar kwallon kafa ta duniya, ta gaza a gasar da aka yi a 2006 da 2010. Kazalika ta fadi a karawar rukuni-rukuni a 2014. Rashar ta koma gida tun farkon karawa a gasar zakarun Turai na 2012 da kuma 2016. A saboda haka jikin magoya bayansu ya yi sanyi a yanzu; kuma tsohon dan wasan kungiyar Schalke Roman Neustädter ma baya cikin tawagar bana.
Ajin matasa
Koda yake wasu na tababa kan tasirin wasannin bazara, kasar New Zealand na farin cikin damar da ta samu na karawa da kasashe a wannan lokaci. Kasar ta na fatan samun tagomashi irin wanda ta samu a karawar da ta yi da Italiya a 2010 inda suka tashi 1-1 lokacin gasar kwallo ta duniya a kasar Afirka ta Kudu a wancan lokaci.
Alamun wata nasara ga Portugal?
Zakarun nahiyar Turai sun dunguma zuwa Rasha. Kungiyar Fernando Santos ta dauki dunkkanin hazikanta, abin da ake ganin ta na iya cancantar zuwa zagayen karshe a birnin Saint Petersburg, ko ma su dauki kofi. Sai dai akwai masu ganin tawagar kasar Mexico ka iya zama masu kayar kifi a wuya.
Gwarzaye masu hatsari
Tawagar kasar Mexico dai na daga cikin manyan tawagogi a wannan gasa saboda dukannin jarumansu na ciki. Ko da yake ana iya cewa mai tsaron gidansu Guillermo Ochoa sabon yankan rake ne, amma akwai masu tsare baya da suka hada da Hirving Lozano da Carlos Vela. Su ma tsoffin hannu irinsu Rafael Marquez da Oribe Peralta, za su taimaka daga bayan fage.
Jamus
Hasashen marubuta na cewa Jamus ce za ta yi zarra a rukunin B. sai dai ‘yan wasan kasar uku ne kadai daga wadanda suka buga a gasar duniya ta 2014 ke cikin wannan tawagar. ‘yan wasan su ne: Skhodran Mustafi da Matthias Ginter da kuma Julian Draxler. Wasu matsan ne za su maye gurbin wadande ke hutun bazara, inda ake sa ran su burge Kocin kasar Joachim Löw.
Baje-kolin shararrun 'yan kwallo
Da farko dai Koci Joachim Löw (na biyu daga hagu) bai da karsashi a wannan gasar. Sai dai bayan fafatawa da kungiyar Denmark da kuma ta San Marino, ya sake samun kwarin gwiwa, inda ya ke ganin wata dama ce 'yan wasan za su samu ta fuskar gogewa da karuwar fahimtar wasa ga musamman sabbin dauka da kuma shiga fage.
Waiwaye cikin shekaru 12 baya
A shekara ta 2005, kasar Jamus ce ta karbi bakuncin gasar nahiyoyi, inda a karon farko ta fafata da kasar Australiya. Gasar da aka yi a birnin Frankfurt, ta kayatar da ci 4-3 inda Jamus ta yi nasara. Duk da cewar Jamus din na da zakaru cikin tawagarta da ke wasa a nahiyar Turai, da dama daga cikinsu na zaune ne a kasar Australia.
Dan wasa Tim Cahill
Tim Cahill, dan shekaru 37, ana iya cewa zakara ne da ya yi suna a tawagar ‘yan wasan. Tsohon dan wasan kungiyar Everton ya taba taka leda a New York da kuma China kafin daga bisani ya karkare a birnin Melbourne a gasar Lik-Lik. Cahill ya kuma taba buga kwallo a kungiyar kasar Australiya a 2005 da 2006 da 2010 da kuma gasar duniya ta shekarar 2014.
Zakarun nahiya fiye da sau guda
Kungiyar da ake iya cewa ta sami nasarori a baya-bayan nan, ita ce ta kasar Chile. ‘’El Roja’’ shi ne ya yi nasara a gasar nahiya ta Amirka da aka yi a 2015 da 2016. Dan wasan ya yi nasara kan Lionel Messi a zagayen karshe na wasanni. ‘Yan kungiyar kwallon kasar, karawa da su sai an taru.
Matasan 'yan kwallo masu jini a jika
A baya kungiyar kwallon kafa ta kasar Kamaru, kungiya ce da ta yi tashe a fagen tamaula. Zakaran kungiyar Samuel Eto’o yanzu ya yi murabus daga murza leda, kuma tsohon dan wasan nan na Bundesliga Joel Matip da kuma Erik Maxim, duk ba su cikin tawagar kasar a yanzu. Amma duk da haka ana ganin kasar ta Kamaru ta za iya samun galaba a gasar nahiyoyin da za a yi a Rasha.
Likafar dan Afirka ta yi gaba
Fitattun ‘yan wasan da ake ji da su a bagaren Jamus, su ne da tsohon dan wasan na Stuttgart wato Georges Mandjeck da kuma Jacques Zoua (da ya fito a hoto). su duka sun fafata kuma suka ci gasar zakarun nahiyar Afirka da aka yi cikin watan Janairu.