1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamitin Sulhu zai gana kan rikicin Libya

Yusuf BalaFebruary 17, 2015

Wannan tattaunawa dai ta kwamtin na Majalisar Dinkin Duniya ta biyo bayan hotunan bidiyo na kisan wasu Misiriwa mabiya addinin Kitrista da kungiyar IS ta yi a ranar Litinin.

https://p.dw.com/p/1EdRv
Libyen Islamisten Demo in Bengasi 31.10.2014
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Hannon

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar zai ganawar a gobe Laraba kan rikicin kasar Libya bayan da mayakan IS suka yanka wasu Misiriwa Kirista 21. Cikin wadanda zasu zauna a wajen taron har da ministan harkokin wajen Masar kamar yadda wasu jami'an diflomasiya suka bayyana a yau Talata.

Wannan tattaunawa dai ta biyo bayan hotunan bidiyo na kisan wadannan Misiriwa da kungiyar IS ta yi abin da ya sanya Masar kai farmaki na ramuwar gayya kan mayakan na IS da ke a Libya a ranar Litinin.

Sameh Shoukry da ke zama ministan harkokin wajen na Masar na birnin New York inda zai wata ganawa da mambobin kwamitin sulhun da wakilan kasashen Larabawa kamar yadda jami'an diflomasiyar suka bayyana.

Kasar dai ta Masar ta bukaci Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniyar ya fitar da wani shiri na kawancen kasashen duniya da zasu tallafa a kawo karshen rikicin da kasar ta Libya ta fada inda fada tsakannin kungiyoyi daban-daban na masu tada kayar baya ya jefa kasar cikin rudani.