Kwanaki 100 na kamun ludayin Zuma a AU
January 22, 2013Sakatariyar zartaswa ta kungiyar Gamayyar Afirka Nkosazana Dlamini-Zuma ta cika kwanaki 100 a kan kujerar shugabancin AU. Ita dai Dlamini-Zuma mai shekaru 63 da haihuwa, mace ce da ta san makamar aiki a fannin dipolomasiya. Ko da a rikicin tawaye da aka yi fama da shi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma wanda kasar Mali ke fama da shi yanzu haka, sai dai aka yaba kamun ludayinta. Daya daga cikin masu jinjina mata kuwa, shi ne Alex vines, darektan da ke kula da al'amuran Afirka a cibiyar tuntuba ta Think Tanks Chatham House ta Burtaniya.
"Ta nuna hangen nesa a lokacin da ta fito fili ta nuna cewar Afirka ba ta da karfin tinkarar kalubalen tsaro da Mali ta samu kanta a ciki. Ita da masu shiga tsakanin da kuma manzanninta na musamman sun baiyana a birnin Alkahira cewa Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka ba su da wasu kwararan kayan yaki na fattattakar masu kishin addini. Saboda wannan dalili ne ta goyi bayan shigar sojojin Faransa a kasar mali, a daidai lokacin da ya fito fili cewa masu kishin addinin sun durfafi Bamako babban birni."
Rawar Zuma a rikin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
A game da rikicin tawayen Jamhuriyar Afirka ta stakiya ma dai, ta fito balo-balo ta baiyana cewa Kungiyar Gamayyar Afirka ba za ta amince da duk wata gwamnati da 'yan tawaye za su kafa ba, ko da hakarsu ta kifar da François Bozize ta cimma ruwa.
Ita Nkosazana Dlamini-Zuma ce ta ruwa da tsaki wajen ganin cewar kasar ta haihuwa wato Afirka ta kudu ta tura da dakaru Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin ja wa 'yan tawayen Seleka burki. A cewar Ulf Engel, kwararren a al'amuran da suka shafi nahiyar Afirka a jami'ar Leipzig da ke nan Tarayyar Jamus, Dlamini Zuma ta dora ne kan inda magabatanta suka tsaya.
"Da farko dai ya kamata a lura cewa ta na assasa wasu manufofi da tsohon sakataren zartaswar Au Jean Ping ya girka. Wannan ya na daga cikin abubuwan da Au ta gada. Da yawa daga cikin al'amura ba huruminta ba ne. A daya hannun kuma an samu ci gaba a sigar tafiyar da Au. Ta kawo wani salo na tafiyarwa da ya sha babban da na baya."
Dlamini-Zuma na bai wa al'amuran da suka shafi cin zarafin mata da yara kanana a lokacin tashe tashen hankula mahimmaci. Amma kuma akwai wadanda ke yi mata hannunka mai sanda game da babban kalubalen da ya kamata ta fuskanta: wato rikie rikice da ke ci wa nahiyra Afirka tuwo a kwarya. Saboda haka Mehari Maru, baban jami'in da ke ba da sharhi a fannin tsaro ya ce kamata ya yi zumar da dukufa wajen samar da zaman lafiya mai dorewa a daukacin kasashen n ahiyar Afirka.
Rahoto cikin sauti na kasa
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi