Ukraine na gasa wa Rasha aya a hannu-Wolodymyr Selensky
December 20, 2022Talla
A cikin wani jawabinsa na kowane dare ga 'yan kasar, Shugaba Selensky, ya ce fiye da sojin Rasha 900 ne suka kwanta dama a yakin, yana mai cewa nan da wasu 'yan lokuttan za su kasance dubu daya.
Wolodymyr Selensky ya zargi Rasha da bata lokaci wajen yakin da ke ja mata mummunan asarar dukiyoyi da na rayuka, duk da kokarin da take na kare manufofinta a yankin.
A ranar 24 ga watan Febrairun wannan shekarar ne Rasha ta kaddamar da mamaya kan makwabciyarta Ukraine, inda a wannan Talatar yakin na Ukraine ke cikja kawanaki 300.