1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliya ta halaka mutune a Kwango

May 5, 2023

Sama da mutane 130 sun halaka a kudancin lardin Kivu da ke jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya janyo ambaliya.

https://p.dw.com/p/4Qy8u
DRK Kongo Erdrutsch Unwetter Starkregen
Hoto: REUTERS

Wani  jami'in gwamnati da ke lardin na kudancin Kivu wanda ke kusa da iyakar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Ruwanda ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da aukuwar lamarin, inda ya ce an tafka asarar ruyukan daruruwan mutane kuma ana ci gaba da kididdige wadanda ambaliyar ta ritsa da su. Har ila yau wani gidan rediyo da ke lardin na Kivu ya ruwaito wani dan majalisar dokoki, ya tabbatar da mutuwar mutane 150 da kuma wadansu da dama da suka yi batan dabo. Kazalika wani jami'in ceto ya shaidawa AFP din cewa, sun yi nasarar tsamo gawarwakin mutane 68 kuma ana ci gaba da lalube. Har kawo yanzu ana jiran kididdiga daga gwamnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon, dangane da wannan lamari da ba shi ne na farko ba a lardin na Kivu da dama ke fama da matsalar tsaro.