1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta bukaci jinkirta sakamakon zaben Kwango

Abdul-raheem Hassan
January 18, 2019

Kungiyar tarayyar Afirka ta bukaci hukumar zaben Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta dakatar da fitar da sakamakon zaben shugaban kasar na karshe, sakamakon yadda ake shakku.

https://p.dw.com/p/3Bkoa
Äthiopien Moussa Faki Kommissionsvorsitzender Afrikanische Union (AU)
Hoto: Getty Images/AFP/S. Maina

Martin Fayulu wanda shi ne ya zo na biyu a zaben ya kalubalanci nasarar abokin hamayyarsa Felix Tshisekedi, tare da neman hukumar zabe ta sake kidaya kuri'un da ya ke ikirarin nasara. Kungiyar AU na son gani an dakatar da fitar da sakamakon zaben da aka tsara yau Juma'a, matakin ya biyo bayan taron da shugabaninta suka gudanar a birnin Addis Ababa na Kasar Habasha a kan sakamakon zaben da ya ba nuna Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya yi nasara.