1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kwango:'Yan takara biyar za su gudanar da zanga-zanga

December 23, 2023

Gamayyar 'yan takarar shugabancin kasa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango guda biyar, sun sanar da aniyarsu ta gudanar da zanga-zangar lumana a babban birnin kasar Kinsasha.

https://p.dw.com/p/4aWpw
Hoto: Paul Lorgerie/DW

Gamayyar 'yan takara biyar daga cikin 19 da ke neman shugabancin kasa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango guda biyar, sun sanar da aniyarsu ta gudanar da zanga-zangar lumana a babban birnin kasar Kinsasha ranar 27 ga wannan wata na Disamba da muke ciki.

'Yan takarar daga jam'iyyu biyar sun fitar da sanarwar a yau Asabar, inda suka ce sun dauki wannan mataki ne domin nuna fushinsu kan yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar da ke tattare da kura-kurai da kuma tafka magudi.

A wani martanin da ya yi tun da fari kan yadda aka gudanar da zaben yayin wani taron manema labarai a birnin Kinsasha, Denis Kadima da ke zaman shugaban Hukumar Zaben kasar CENI ya yi watsi da zarge-zargen 'yan takarar da ke adawa da sahihancin zaben da kuma masu sanya ido na kasa da kasa.