An kamalla binciken asalin corona
February 10, 2021Tawagar Hukumar Lafiya ta Duniya da aka tura birnin Wuhan na China don gudanar da binciken corona, ta baro kasar a wannan Laraba, bayan ikirarin samun bayanan da suka je nema a game da asalin cutar. Jagoran tawagar Peter Daszak , ya ce, yanzu sun gano inda aka dosa a game da musababbin cutar dama tabbatar da asalinta.
Tun dai bayan bullar cutar corona a Disambar 2019, ake zargin cewa, cutar ta bulla bayan sakaci na barin yoyon wani sinadari a dakin gwaji a Wuhan, akwai masu cewa an yada cutar bayan cin naman jemage da ake siyarwa a wata kasuwa a Chainan da dai sauransu, batun da gwamnatin Chainan ta sha musawa.
Ana fatan ganin wannan binciken na Hukumar Lafiya zai taimaka kwarai a gano bakin zaren warware takaddama kan annobar corona da kawo yanzu tayi sanadiyar rayuka sama da miliyan biyu tare da durkusar da tattalin arzikin duniya.