1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwarya-kwaryar tsagaita wuta a Siriya

Umaru Aliyu/USUSeptember 13, 2016

Rahotanni daga kasar na cewa kura ta lafa a fagagen daga musamman a yankunan man'yan birane kamar Damaskus da Aleppo da Idleb.

https://p.dw.com/p/1K1Xj
Syrien Zivilbevölkerung in Aleppo
Hoto: Reuters/A. Ismail

Gwamnatin kasar Siriya ta ce za ta yi watsi da duk wani kayan tallafi zuwa yankin Aleppo ba tare da an sanar da ita ba, ko ya bi ta hanyar Majalisar Dinkin Duniya, musamman kayan agaji da ya fito daga kasar Turkiya kamar yadda rahotanni na kafafan yada labarai ya nunar.

Ma'aikatar harkokin wajen Siriya ta bada wannan bayani a cewar kamfanin dillancin labarai na SANA. Wannan jawabi dai na zuwa ne bayan da wasu rahotanni ke cewa, akwai jirgin kayan agaji da ya nufi birnin na Aleppo daga Turkiya a ranar Talatan nan, abin da ke zuwa sa'oi bayan da shirin tsagaita bude wuta ya fara aiki bayan shiga tsakanin Amirka da Rasha.

Amma dai ga bisa yakin, an ruwaito daraktan kawancan kungiyoyin farar hula masu sa'ido a yakin kasar ta Siriya, Rami Abdel Rahamen na cewa baya ga 'yan rokoki da aka harba a yankin kudu a dai dai lokacin da yarjejeniyar ta soma aiki, a takaice za a iya cewa komai ya lafa.

Sakataran harakokin wajen Amirka John Kerry ya bayyana wannan yarjejeniyar tsagaita wuta a matsayin wata dama ta karshe ta ceto kasar Siriya daga halin yakin da take ciki. Har ya zuwa yau dai 'yan tawayen kasar ta Siriya ba su bada na'am dinsu ba ga yarjejeniyar, wacce a bangaren ta gwmnatin kasar ta Siriya, ta bayyana amincewarsa da tsagaita wuta har na tsawon mako daya a duk fadin kasar.

Syrien Aleppo Free Syrian Army
Hoto: picture-alliance/dpa/E. Sansar

Mahukunta a kasar Rasha sun bukaci takwarorinsu na Amirka da su ja kunnen masu kunnen kashi da ke neman illa ga shirin tsagaita wuta a Siriya, wadanda suka ki tsaida yakar sojan gwamnati, inda ta ce ayyukansu za su iya maida hannun agogo baya, a kokarin da mahukuntan na Moscow da Washington ke yi na ganin shirin tsagaita wuta ya samu gindin zama a kasar ta Siriya.

A cewar ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Rasha ya zama dole duk masu ruwa da tsaki a harkar tsagaita wutar, musamman Amirka dole ta ja hankali na wadanda take marawa baya. Kada a bari wani ya yi amfani da matakan harzuka zukata ya gusar da mafarkin da a ke yi na neman matakan kawo sauyi a kasar ta Siriya a siyasance.

Wasu kungiyoyi dai sun bayyana cewa ba zai yiwu ba, su nesanta kansu da Jabhat Fatah al Sham, wacce a baya aka fi sani da Al-Nusra Front, kungiyar da ke alaka da manyan 'yan ta'adda na duniya kamar Al-ka'ida.