1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwaskwarimar tsarin nukilya a Rasha

September 25, 2024

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce a dole hukumomin kasar su sauya tsarin da kasar ke aiki da shi a yanzu na kawar da barazanar nukilya daga abokan gaban Rasha da kawayenta

https://p.dw.com/p/4l4wA
Atomraketen Russland
Hoto: ARTYOM KOROTAYEV/AP/picture alliance

Shugaban kasar ta Rasha da ya yi jawabinsa a wannan Laraba, inda ya ce a ganin irin sauyin da ake samu daga bangaren makiya, ya zama wajibi Rasha ta dau duk matakai da za su kawar da duk abinda zai iya zama barazana ga kasar ko da kuwa makamin nukiliya ne. Vladimir Putin yace idan aka duba yadda halin zaman dar-dar da yanzu haka duniya ke ciki, akwai babban nauyi da ke kan rundunar sojan Rasha na tabbatar ta kawar da duk wata barazana ga kasarsu dama kasashe kawayen Rasha. Inda yace daga cikin matakan da suka wajaba sune, fisnkatar baranar soji ta kibtawa da bisimmilah, kuma bawai kan Rasha kadai ba yakamata har duk kawayen Rasha a samarsu wannan matakin da zai iya aiki cikin hanzari.