Kyaftin Traore ya ce a kwantar da hankali
October 4, 2022Kyaftin Traore ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewar wannan aikin na ECOWAS ko CEDEAO, ana yin sa ne don tuntubar sabbin mahukuntan Burkina Faso a matsayin wani bangare na tallafin da kasashen yammacin Afirka suka bayarwa.
A daren Litinin zuwa wannan Talata ne wasu kungiyoyi suka kafa shingaye a tsakiyar birnin Ouagadougou domin nuna adawa da zuwan tawagar kungiyar ta ECOWAS. Sannan, an ta yada sakonni a shafukan sada zumunta ne neman kawo wa ziyarar cikas. Dama kungiyar ECOWAS ta saba shan suka a kasashen yammacin Afirka bisa ga tsarinta idan aka yi juyin mulki ba tare da la'akari da muradun jama'a ba.
Sai dai Kyaftin Traore ya yi alkawarin mutunta alkawuran da magabacinsa ya yi wa kungiyar ECOWAS kan shirya zabe da kuma dawowar farar hula kan karagar mulki nan da watan Yulin 2024.