1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Dadadden tarihi na hulda tsakanin Jamus da Afirka

Mohammad Nasiru Awal
September 24, 2021

Gwamnatin Jamus karkashin jagorancin Angela Merkel ta mayar da hankali sosai a kan yammacin Afirka. Kama daga ayyukan raya kasa da batun bakin haure har zuwa batun tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/40pUR
"Compact with Africa"-Konferenz in Berlin
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Gwamnatin Jamus musamman ma karkashin jagorancin shugabar gwamnati mai barin gado Angela Merkel ta taka rawa sosai a Najeriya wajen tallafi a fannoni da dama da suka hada da na tsaro, tattalin arziki da kuma bunkasa al'adu na jama'a. Jamus din dai kan nuna cewar tana da taushi da yakana wajen martaba muradun al'ummomi na duniya,kwatankwacin yadda ga misali ta amsa maido da wasu kayayyakin tarihin Birnin Benin na Jihar Edo a Najeriyar, kimanin dai-dai har dubu bakwai, da tarihi ya nunar a shekaru aru aru turawan na Jamus sun yi awon gaba da wadannan kayayyaki da ke zaman ababen tinkaho ga al'ummar Jahar ta Edo.

Al'ummar arewacin Najeriya ma sun ce babu wata kasa a nahiyar Turai ko kuma na sauran sassan duniya da suka yi ayyukan raya kasa da dama da kuma ayyukan jin kai da ya taba rayuwar al'umma da ke tsananin neman taimako kamar gwamnatin kasar Jamus karkasnin mulkin Angela Markel.

Maraba da babbar bakuwa daga Jamus. Angela Merkel a Nijar a 2019. A dama Brigi Rafini
Maraba da babbar bakuwa daga Jamus. Angela Merkel a Nijar a 2019. A dama Brigi RafiniHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

A yayin da shugabar gwamnatin ke bankwana da iko, a Jamhuriyar Nijar ma al'ummar kasar ce ke yabawa bisa ga moriyar da suka ci a huldar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu musamman a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan tun lokacin hawan ikon Angela Merkel .

Akwai kuma kyakkyawar danganta tsakanin Ghana da Jamus tun bayan samun 'yancin kan Ghana a shekara 1957 daga hannu turawan mulkin mallaka. Kyakkyawar alakar da ke tsakanin Ghana da Jamus, ta ba da damar samun kwakkwaran hadin kai a fannonin kasuwanci da saka hannun jari, shirye-shiryen musayar ilimi da ayyukan al'adu. Kazalika kasashen biyu sun kulla huldar siyasa ta kut -da -kut.

Duk da cewar Ghana ta ci gajiyar dimbin saka hannun jari da ayyukan kasuwanci na tattalin arziki daga Jamus. Kasar ta jawo masu zuba jari daga Jamus a fannonin gine -gine, aikin gona, masana'antu da ayyuka.

Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier da Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana a birnin Accra a 2017
Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier da Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana a birnin Accra a 2017Hoto: DW/Isaac Kaledzi

Ziyarar shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier zuwa Ghana a watan Disambar shekara ta 2017, na zama babban matsayi a dangantakar Jamus da Ghana domin kuwa a lokacin ne ya kaddamar da shirin gwamnatin Jamus na taimaka wa bakin haure da suka zabi barin Jamus da son rai don samun ayyukan yi da abubuwan da ake so a kasashensu, wanda kawo yanzu ya taimaka wa daruruwan jama'a don samun kyakkyawar makomar rayuwa.

Da kasar Kamaru kuwa dangantaka da alaka da ke tsakaninta da Jamus na ci gaba da tasiri a fannoni dabam-dabam musamman fannin ilimi. Kamaru ta kasance kasa ta farko a Afirka mai yawan dalibai da ke karatu a Jamus kawo yanzu. Jamus ce kasa ta farko da ta mallaki Kamaru a shekara ta 1884 zuwa 1916 daga bisani Turawan mulkin mallakar Faransa da hadin gwiwar Ingila suka kori Jamus, amma duk da hakan Jamus ba ta yi kasa a gwiwa ba, ta ci gaba da tallafa wa Kamaru.