1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaAfirka

Afirka: Barazanar kyandar biri

August 14, 2024

Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Afirka, ta ayyana cutar kyandar biri da ke kara yaduwa a matsayin kalubalen gaggawa na lafiya a nahiyar. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce dubban mutane sun kamu da cutar.

https://p.dw.com/p/4jTTE
Afirka I Annoba I Kyandar Biri | Riga-kafi | Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Kasashen nahiyar Afirka, na fama da annobar kyandar biriHoto: AP/picture alliance

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO din ta ce, galibin wadanda suka kamu da cutar ta kyandar biri na a birnin Goma na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Hukumar ta WHO ta bi sahun kungiyar Tarayyar Afirka AU, wacce tun da fari ta ayyana cutar ta kyandar biri a matsayin annoba. A cewar WHO din, tana ci gaba da nazari wajen duba yiwuwar ayyana cutar kyandar birin a matsayin gagarumar annoba da ke bukatar agajin gaggawa. Cutar da ake kira da Monkeypox da Turancin Ingilishi dai, na ci gaba da lakume rayuka a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. An fara gano cutar a shekarar 1970 a Kwango, wanda daga bisani ta yadu zuwa wasu kasashe. A dan kwarya-kwaryar jawabin da ya gabatar gabanin taron gaggawa na WHO din, shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce suna fadi tashin dakile yaduwar cutar a birnin Goma da ma sauran sassan Kwangon da nufin dakile yaduwar cutar a kasashe makwabta da suka hadar da Burundi da Kenya da Ruwanda da kuma  Yuganda da tuni aka samu rahotannin bullarta.

Afirka I Annoba I Kyandar Biri | Riga-kafi
Kokarin samar da isasshiyar allurar riga-kafin cutar kyandar biri da ke barazana a AfirkaHoto: Joe Raedle/AFP/Getty Images

To amma al'ummar garin na Goma sun shaidawa DW cewa, ba su da masaniyar matakan da hukumomin ke dauka dangane da annobar. Dakta Trésor Hamiri Hemedi kwararren likita ne a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango, kuma ya ce sanya idanu a iyakokin Kwango na da matukar tasiri. Shugaban hukumar ta WHO ya ce, akwai matakan da suka bijiro da shi na riga-kafin dakile yaduwar cutar tare da amincewa da hukumomi biyu da za su dau ragamar rarraba ta. Cutar kyandar biri na yaduwa daga mutum zuwa dabba da kuma mutum zuwa mutum, ta hanyar cudanya da juna. Dakta Rosamund Lewis ita ce babbar daraktan da ke kula da sashen dakile yaduwar cutar cikin gaggawa, ta ce WHO na bibiyar yaduwar cutar a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. A baya dai kwamitin Hukumar Lafiya ta Duniyar WHO ya ayyana dokar ta-baci da kuma bukatar daukin gaggawa kan annoba har guda bakwai tun daga shekara ta 2009, wadanda suka hada da murar tsuntsaye da shan inna da Ebola da Zika Virus da Ebola har sau biyu da COVID-19 da kuma kyandar biri.