Firaministan Girka cikin tsaka mai wuya
November 7, 2022Talla
Jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi ta tsohon firaministan Alexis Tsipras Syriza, ta bukaci a ba da haske kan wannan al'amari kafin zabuka masu zuwa da aka shirya yi a lokacin rani na shekara ta 2023. Jam'iyyar ta adawa ta Girkan ta ce tana tunanin yin amfani da kuri'ar yankan kauna a majalisar dokoki don adawa da gwamnatin Conservative, wadda ke da rinjaye a majalisar. Daga cikin wdanda ake zargin hukumar leken asirin Girkan ta rika satar sauraran bayyanan wayoyinsu na hanu har da tsohon firaministan kasar Antonis Samaras da wasu 'yan jaridar na adawa da kuma wasu ministocin.