1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labaran Afirka da suka shiga jaridun Jamus

Usman Shehu Usman
May 5, 2023

Jaridun na Jamus sun yi nazarin irin makaman da ke yin tasiri a rikicin Sudan da rangadin aikin shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a gabashin Afirka.

https://p.dw.com/p/4Qxhk
Äthiopien | Bundeskanzler Scholz in Addis Abeba
Mousa Faki Mahamat da Olaf ScholHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Za mu fara da sharhunan jaridun na wannan makon da jaridar Die Tageszeitung wadda da ta buga labari mai taken" Jamus ta cika Sudan makil da makamai". Jaridar ta ruwaito wani masanin kasar Sudan mai suna Roman Deckert wanda ke bayyana yadda kasashen duniya musamman ma dai Jamus ke tunkarar rikicin Sudan.

Tsare-tsare na inganta kayan yaki bisa manufar kare kai 'yan gudun hijira, da kuma yin watsi kan fafutikar kungiyoyin farar hula da ke adawa da mulkin kama-karya, wanda kasashen yamma suka yi da sunan nuna girmamawa ga janar-janar da ke kan mulki, to yanzu shi ne abin da kasashen ke girba a cewar Roman Deckert.

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel ta duba ziyarar shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ne a yankin gabashin Afirka. Jaridar ta ce a ziyararsa Scholz ya tsara tattaunawa da Firimiyan Habasha Abiy Ahmed sai kuma William Ruto na kasar Kenya.

Da jaridar ta duba matsayin shugaban kasar Kenya, ta ce ba gwani ba ne a Kenya, amma ana yaba shi a yammacin duniya. Ta ci gaba da cewa Shugaba William Ruto dan shekaru 56 da haifuwa wani irin masoyin kasashen yamma ne kama daga shugabannin kasashe da jami'an diflomasiyya. Ana ganinsa a matsayin mai kuzari, mai aiwatarwa kuma, uwa uba, mafi kusanci fiye da duk magabatansa.

Ruto yana matukar kula da dangantakar tattalin arzikin kasarsa da harkokin siyasa. Sai dai in an tuna baya, Ruto ba abin koyi ba ne sai dai kawai ace abokin tarayya. Rikicin Sudan dai yana daga cikin abin da shugaban gwamnatin Jamus ya  tattaunawa da mahukuntan Kenya da Habasha masu makobtaka da Sudan.