Labarin Wasanni: 06.11.23
November 6, 2023Sakamakon wasan Pirimiya da aka kara a Ingila, inda aka yio cece-kuce game da kwallon da Newcastle ta jefa a ragar Arsenal 1 da nema, inda ake tararrabi kan cewa kwallon ta fita waje kafin dan wasan ya dawo da ita cikin fili lamarin da ya dauki lokaci kafin tantancewa. Ita kuma Manchester City ta yi raga-raga da Bouremouth 6 da 1, haka Manchester United ta bi Fulham gida ta doke ta 1 mai ban haushi, ita ma Crystal Palace ta bi Burnley gida ta doke ta 2 da nema.
A wasan La Liga da aka kara a Spain, kungiyar Real Madrid ta tashi babu jefa kwallo a raga da Rayo Vallecano, sannan Barcelona ta bi Real Sociedad har gida ta lallasa ta 1 da nema, kana Ath. Bilbao ta bi Villarreal gida ta doke ta 3 da 2, ita kuwa Valencia ta doke Granada 1 da nema.
A wasan Bundesliga na Jamus, Bayern Munich ta bi Dortmund har gida ta doke ta 4 da nema, kungiyar Heidenheim ta samu galaba kan Stuttgart 2 da nema, FC Kolon da Bremen sun tashi 1 da 1, Freiburg da Mönchengladbach sun tashi 3 da 3, inda kungiyar Frankfurt ta bi Union Berlin gida ta lallasa ta 3 da nema. Wasan da Mainz ta doke RB Leipzig 2 da nema.
Duk da dokar haramta cusa siyasa a harkokin wasannin da kundin wasanni na kasa da kasa ya tanada, kungiyoyin wasanni da 'yan wasannin kansu a fadin duniya, na ci gaba da karya wannan doka ,musamman dangane da yakin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin Falasdinawa da Isra,ila, lamarin da yayi matukar yin tasiri a harkar wasanni ta duniya.
Kwanaki bayan kasar Afirka ta Kudu ta lashe kofin duniya na zari-ruga da aka kammala a Faransa, yanzu kuma kasar ta Afirka ta Kudu tana ci gaba da taka rawar gani a wasan neman cin kofin duniya na Cricket da kasar Indiya take daukan nauyi, kuma duk da cewa mai masaukin bakin ta samu galaba kan Afirka ta Kudu a wasan da suka kara, amma Afirka ta Kudu ta samu tsallakawa zuwa wasan kusa da na karshe inda ranar Jumma'a mai zuwa za a kece raini tsakanin Afirka ta Kudu da kasar Afghanistan.