Shirin Labarin Wasanni
October 12, 2020Rafael Nadal dan kasar Spain din dai, ya samu nasara bayan doke Novak Djokovic dan kasar Sabiyan da ci shida da nema, shida da biyu da kuma bakwai da biyar. Wannan na zaman karo na 13 da Nadal ya lashe gasar, ya kuma ce ya zage iya karfinsa domin samun nasarar. A bangaren mata kuwa Iga Swiatek 'yar kasar Poland ta samu galiba kan Sofia Kenin 'yar Amirka da ci shida da hudu da kuma shida da daya. Yanzu haka dai Iga Swiatek ta tashi daga matsayi na 37 a jerin gwanayen tennis na duniya zuwa matsayi na 17, bayan nasarar da ta samu a karshen makon.
A karshen makon ne kuma aka kara wasannin kasashe na hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasashen Turai UEFA, inda Jamus ta samu nasara a kan Ukraine da ci biyu da daya kana Spain ta doke Switzerland da ci daya mai ban haushi. Poland da Italiya sun tashi babu ci, haka labarin yake tsakanin Faransa da Potugal, kana Rasha da Turkiyya sun tashi daya da daya, inda Finland ta samu nasara kan Bulgaria da ci biyu da nema, yayin da Norway ta lallasa Romaniya da ci hudu da nema, Croatia ta doke Sweden da ci biyu da daya.
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da ke Jamus Jerome Boateng ya bukaci ganin 'yan wasan kungiyar sun kara zage damtse domin kare nasarorin da kungiyar ta samu na lashe dukkanin gasar da ta shiga da suka hadar da kofin zakarun kasashen Turai. Kungiyar Real Madrid da ke Spain kadai ta samu nasarar kare kambun na zakarun nahiyar Turai a shekara ta 2017 da 2018 tun daga shekarar 1992, abin da dan wasan Boateng yake fata kungiyarsa ta Bayern Munich ta samu ita ma ta kwatanta.
Shugaban hukumar kula da wasannin lig na Ingila da ake kira Premier lig, Rick Parry ya yaba da matakin tabbatar da samun sauye-sauye a gasar lig din da kungiyoyin Liverpool da Manchester United suka gabatar. Tsarin da ke cike da cece-kuce dai ya hadaar da rage yawan kungiyoyin gasar daga 20 zuwa 18. Babban jami'in yana ganin matakin a matsayin wata damar samun gagarumin sauye-sauye tsawon shekara da shekaru da suka gabata game da gasar Premier lig ta Ingila wadda ke daukar hankali a ciki da wajen kasar.
Suma a nsau bangaren kasashen nahiyar Afirka sun fafata a wasannin kwallon kafa dabam-dabam a karshen makon da ya gabata.