1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni 18.07.2022

Lateefa Mustapha Ja'afar M. Ahiwa
July 18, 2022

A cikin shirin muna tafe da rahoto kan matsalolin da kwallon kafa ke fuskanta a Nijar da halin da ake ciki a gasar cin kofin kwallon kafa na matan Afirka da ke ci a Moroko.

https://p.dw.com/p/4EIbb
Fußball | Women s Cup of Nations | WAFCON | Uganda - Marokko
'Yan wasan kasar Moroko a gasar kwallon kafa ta mata zallaHoto: Tobi Adepoju/Shengolpixs/IMAGO

Kasashen Koriya ta Kudu da Ostireliya da Indonesiya da Qatar, sun mika takardun neman maye gurbin kasar China wajen karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Asiya da za a gudanar a badi.  Hukumar kula da kwallon kafa ta kasashen Asiyan ce ta sanar da hakan, inda aka bayyana ranar 31 ga watan Agusta mai zuwa a matsayin ranar karshe ta kammala mika takardunsu kafin kwamitin ya tantance tare da bayyana kasar da za ta karbi bakuncin gasar a ranar 17 ga watan Oktoba. A watan Yuni da Yulin shekara mai zuwa ta 2023 ne dai aka tsara China za ta karbi bakuncin gasar, sai dai kuma kasar ta gaza cimma tsarin yaki da annobar COVID-19.

Kasashen Jamus da Ingila da Spain da Ostiriya da Sweden da Faransa da kuma Holland, sun samu nasarar kaiwa ga wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin kwallon kafa na mata ta kasashen nahiyar Turai. A yammacin yau ne dai za a fafata wasannin karshe na zagaye na biyu tsakanin Iceland da Faransa kana a kece raini tsakanin Italiya da Beljiyam. Za dai a fafata wasannin daf da na kusa da na karshe din ne a ranakun Laraba da Jumma'a na wannan mako da muke ciki. Jamus ce dai ta fi samun nasara a gasar, domin kuwa ta lashe kofin har sau takwas tun bayan fara ta a shekara ta 1984.

Europa League Finale | Eintracht Frankfurt - Glasgow Rangers
Kofin kasashen nahiyar TuraiHoto: Andrew Milligan/PA Images/IMAGO

Da yammacin yau ne za a fafata a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin kwallon kafa na mata ta kasashen nahiyar Afirka da ake fafatawa a yanzu haka a Moroko. Wasan farko dai za a fafata shi ne tsakanin Zambiya da Afirka ta Kudu kafin daga bisani kuma mai masaukin baki Moroko ta kece raini da Najeriya. Za kuma a fafata wasan neman zama na uku a ranar Jumma'a kana a fafata a wasan karshe a ranar Asabar da ke tafe. Najeriya ce dai ke kan gaba wajen lashe gasar tun bayan fara ta a shekara ta 1991 inda ta dauki kofin har sau 12. Afirka ta Kudu ce ke biye mata, inda ta dauki kofin sau biyar Kamaru sau hudu kana Ghana ta dauka sau uku.

Muhawara ta kaure a Jamhuriyar Nijar dangane da yadda karfin kwallon kafa a kasar ya koma ga kungiyoyin sojoji da na sauran jami'an tsaro, a yayin da kungiyoyin unguwanni wadanda suka kafa tarihi a kwallon kafar kasar ke ci gaba da mutuwa ko sauka zuwa rukuni na biyu.

Tour de France | Tadej Pogacar gewinnt Etappe
Gwanin tseren keke na Tour de France, Tadej PogacarHoto: David Stockman{BELGA MAG/AFP/Getty Images

A yayin da aka kammala zagaye na 15 na gasar tseren keke ta Tour de France da ke gudana a yanzu haka, Jonas Vingegaard na ci gaba da kokarin karbe kambun tseren keken ta duniya daga Tadej Pogacar da a yanzu haka yake rike da kambun. Annobar Corona dai na ci gaba da bayyana a tsakanin 'yan tseren, inda a yanzu haka aka bayyana cewa akwai wasu 'yan tsere biyu da suka kamu da kwayar cutar. Sai dai wani abu guda da ake korafi a kansa a gasar, shi ne karanci ko ma rashin 'yan tsere daga nahiyar Afirka. Ga misali dan kasar Ruwanda Adrien Niyonshuti ya yi fice a tseren keke, inda a shekara ta 2012 ya wakilci kasarsar a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da aka gudanar a birnin London na kasar Birtaniya. Shi ne bakar fata na farko da ya halarci gasar tseren keke ta hawa tsaunuka ta duniya. Ya samar da makarantar koyon tseren keke a kasarsa, inda a yanzu haka kimanin 'yan tsere 40 ke karbar horo daga gare shi.