Labarin Wasanni: 20.06.2022
June 20, 2022Ana gani cewa Sadio Mané zai maye shahararrren dan wasa Robert Lewandowski dan kasar Poland. Sai dai muddin Lewandowski bai samu wata kungiya ba, akwai yiwuwar Bayern Munich ta fuskanci cikas bayan dawowar dan wasa Sadio Mané. Shi dan kasar ta Senegal na daga cikin 'yan wasa da suka sa kasarsa lashe kofin kwallon na kasashen Afirka a farkon shekara ta 2022.
Bruce Buck zai sauka a matsayin shugaban kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke Ingila, kamar yadda wata sanarwa ta wannan Litinin ta tabbatar. Dan Amirkan zai sauka daga shugabancin a watan Yuni mai zuwa, amma ya ce zai ci gaba da zama a matsayin mai ba da shawara ga kungiyar. Shi dai Bruce Buck yana shugabancin tun shekara ta 2003 kuma zai sauka sakamakon sauyi saboda kungiyar ta fita daga hannun Roman Abramovich hamshakin mai arziki dan kasar Rasha.
Kungiyar kwallon kafar Austaraliya ta Socceroos ta sami damar karawa a gasar cin kofin duniya na FIFA wanda za'a fara a watan Nuwamban bana. Kungiyar ta yi wannan nasarar ne bayan da ta doke Peru a fenarti bayan da kungiyoyin kasashen biyu suka shafe miniti 120 suna fafatawa ba ci ko daya a tsakaninsu. Wannan nasara ta socceroos ta yi tasiri sosai a kasar wanda har yau ba ta taba ci kofin kwallon kada na FIFA ba.
Mykhailo Romanchuk dan Ukraine da ya samu zinare a gasar ninkaya na duniya na mita-800 a kasar Romaniya a yayin da yaki da ke faruwa a kasarsa. Romanchuk wanda lokacin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya ya samu azurfa guda biyu ya ce wannan nasara da yake samu ya sadaukar kan fata na gari ga duniya baki daya. Sannan dan wasan na ninkaya daga Ukraine ya ce zai ci gaba samun horo domin yin nasara a gasar ninkaya da yake halarta.