'Yan awaren Kamaru na barazana ga AFCON
December 20, 2021A daidai lokacin da ake nuna fargaba dangane da yaduwar nau'in Omicron na annobar corona a nahiyar Afirka, kwamitin zartaswa na Hukumar Kwallon Kafa ta Kasashen Afirka ya yanke shawarar kin dage gasar AFCON ko CAN da Kamaru za ta dauki bakunci a watan Janairu mai zuwa. Shugabannin na CAF sun dauki wannan mataki ne bayan barazanar da kungiyoyin kasashen Turai suka yi, na kin barin 'yan asalin Afirka shiga gasar saboda annobar corona da kuma uwa uba rashin iya cike gurbin 'yan wasan a tsakiyar kaka. Ita dai Kamaru mai masaukin baki ta tsaurar matakan yaki da corona, inda ta sha alwashin yi wa kowa gwajin corona kafin ba shi damar halartar filin wasa. Sai dai har yanzu a nata bangare Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ba ta yanke hukunci kan gasar ta AFCON ba, kasancewar baya ga barazanar kowon lafiya akwai kuma ta tsaro. Hasali ma 'yan awaren yankin da ke magana da Turancin Ingilishi a Kamarun, sun haramta gudanar da gasar cin kofin Afirka a yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Yammancin kasar da suke cewa yana karkashin ikonsu . A cikin wata sanarwa da daya daga cikin jagororin kungiyar Ambazoniya Chris Anu ya fitar, ya yi barazanar kai hare-hare yayin gasar musamman wandanda za su gudana a Limbe da ke Kudu maso Yammacin kasar. Tuni dai jami'an tsaron kasar, suka dauki matakan dakile ta'addanci a filin wasan.
Kasar Aljeriya ta lashe gasar kofin kasashen Larabawa da aka karkare a karshen mako a birnin Doha na kasar Qatar, bayan ta doke kasar Tunusiya da ci biyu da babu. Masana harkar tamaula sun dauki wannan gasa a matsayin zakaran gwajin dafi a gasar kwallon kafa ta duniya ta kasar Qatar za ta dauki nayi a watan Disamban badi. A Jamus, wariyar launin fata ya sanya alkali dakatar da wasan da aka yi tsakanin Duisburg da Osnabrück a rukuni na uku na Bundesliga, bayan an shafe rabin sa'a ana wasa. Alkalin wasa Nicolas Winter ya bayyana cewa, ana danganta dan wasan gaba Aaron Opoku da biri daga bangaren 'yan kallo lamarin da ya ki lamunta da shi. Tuni dai aka gano mai goyon bayan da ake zargi da kalaman wariyar launin fatar, kuma aka fitar da shi daga filin wasan. Kulob din na Duisburg dai, ya nemi afuwa dangane da abin da ya faru.
Har yanzu muna Jamus, a wasannin na Bundesliga amma rukunin farko a mako na 17 kuma na karshe a wannan shekara ta 2021. A wasannin da suka gudana a karshe mako, kungiyar Freiburg ta bayar da mamaki ta hanyar lallasa Leverkusen da ci biyu da daya. Nasarar dai, ta ba ta damar shiga sahun ukun farko na teburin gasar. Duk da kasancewarta daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa masu karancin kudin shiga a Jamus hazakar 'yan wasanta ta sa Kevin Schade ya zira kwallon karshe a mintuna na 84 da fara wasa, lamarin da mai hiras da 'yan wasan na Freiburg Christian Streich yake alfahari da shi. Sai dai kungiyar RB Leipzig da ke a matsayi na biyu a kakar bara a Jamus, ta yi abin fallasa saboda daya daga cikin kurar baya a kakar bana wato Armenia Bielefled ta casa ta da cibiyu da nema. Wannan dai ba ya rasa nasaba da rashin alkibla da Leipzig take fama da shi, tun bayan da mai horas da 'yan wasanta Julian nagelsman ya raba gari da ita. A nata bangaren Borussia Mönchengladbach ta yi kunnen doki da Hoffenheim ci daya da daya, lamarin da ya ba ta damar kawo karshen rikicin da kungiyar da ke a matsayi na 14 ke fama da shi. Ita kuwa Bayern Munich tana ci gaba da jan zarenta ba tare da ya tsinke mata ba, bayan da ta yi wa Wolfsburg dukan kawo wuka ci hudu da nema tare da ci gaba da zama a saman teburi da maki 43. Tuni ma Bayern ta samu tabbacin samun kwarya-kwaryar kambun zakara na rabin zango, kasancewar Borussia Dortmund ba za ta iya cike gibin da ke tsakaninsu ba, saboda ta dibi kashinta a hannun Hertha Berlin da ci uku da biyu ma'ana akwai ratar maki tara tsakanin Bayern da Dortmund.
A sauran sakamakon rana ta 17 din kuwa, Union Berlin ta Idoke Bochum da ci daya mai ban haushi. Ita ma Cologne ta yi nasarar lallasa Stuttgart da ci daya mai ban haushi, yayin da Greuther Fürt da ke zama kurar baya ta yi kunnen doki ci daya da daya da Augsburg. Ita kuwa Frankfurt ta lallasa Mainzne da ci daya mai ban haushi, lamarin da ya ba ta damar kasancewa a matsayi na shida a teburin kakar Bundesligar ta bana. Kasar Norway ta lashe gasar cin kofin kwallon hannu na duniya na mata na 2021, bayan da ta doke Faransa a ranar Lahadin karshe a Spain da ci 29 da 22. Kasashe hudu ne dai suka wakilci nahiyar Afirka a wannan gasa, ciki har da Kamaru da Tunisiya da Angola da Kwango, wadanda aka yi waje road da su tun kafin aski ya iso gaban goshi.