1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yadda wasanni suka kaya a karshen mako

Mouhamadou Awal Balarabe
October 7, 2024

Brazil ta lashe gasar cin kofin duniya ta Futsal, ta wasan kwallon kafa da ake bugawa a daki. Manyan kungiyoyin kwallon kafar Jamus, sun kasa tabuka abin kirki a mako na shida na Bundesliga.

https://p.dw.com/p/4lVs7
Bundesliga | Eintracht Frankfurt | Bayern Munich
Gumurzun Eintracht Frankfurt da Bayern MunichHoto: Uwe Anspach/dpa/dpa

Bayern Munich da ta fara kakar wasan Bundesliga ta bana da kafar dama ta yi canjaras uku da uku da Frankfurt a mako na shida, mako guda bayan da ta tashi kunnen doki daya da daya a karawarta da Bayer Leverkusen da ke rike da kambu. Amma mai horas da kungiyar Vincent Kompany ya ce ba wani abin fallasa da 'yan Bayer Munich suka yi, domin sun mamaye Frankfurt. Duk da rashin nasara a wasannin biyun da suka gabata dai, Bayern Munich ta ci gaba da kasancewa a saman teburin Bundesliga da maki 14 kana RB Leipzig da ta samu nasara a kan Heidenheim da ci daya mai ban hasuhi ta samu damar yin kafada da kafada da Bayern din. Eintracht Frankfurt na ci gaba da yin kwanton bauna saboda ratar maki daya kacal ke tsakaninta da 'yan sahun farko, ita kuwa Freiburg da ta yi nasara a kan Werder Bremen da ci daya mai ban hashi tana a matsayi na hudu.

Bundesliga | Bayer Leverkusen | Holstein Kiel
Gumurzun Bayer Leverkusen da Holstein KielHoto: Thilo Schmuelgen/REUTERS

Amma zakaran kwallon kafar Jamus Bayer Leverkusen da ke wasa a gida ta ga ja da janyewa, domin kuwa 'yar baya ga dangi Holstein Kiel ta yi nasarar farke kwallaye biyun da aka zura mata. Wannan lamari dai ya bayar da mamaki, ko da Xabi Alonso da ke horas da Leverkusen sai da ya ce 'yan wasansa ba su dauki abokan karawarsu da muhimmanci ba. Wata tawagar da ba ta taka rawar gani ba, ita ce Borussia Dortmund a gidan Union Berlin da aka lallasa da ci biyu da daya. Wannan lamari ya jefa Dortmund din cikin wani yanayi mai sarkakiya a Bundesliga, kuma ya sha bam-bam da nasarar da ta yi a gasar cin kofin zakarun Turai da take zura kwallaye a raga. A sauran sakamakon wasannin rana ta shida, Wolfbsurg ta samu nasara a kan Bochum da ci uku da daya, yayin da Augsburg ta doke Borussia Möchengladbach da ci biyu da daya. Ita kuwa Mainz ta barza wa St Pauli aya a hannu da ci uku da nema, yayin da Stuttgart ke ci gaba da kwan-gaba kwan-baya bayan da ta tashi wasa kunne doki daya da daya da Hoffenheim.

Premier League | Gumurzun Liverpool | Crystal Palace
Gumurzun Liverpool da Crystal PalaceHoto: Paul Ellis/imago images

A sauran manyan lig-lig na kasashen Turai kuwa, a Ingila Liverpool ke kan gaba a teburin Premier League bayan doke Crystal Palace da ta yi da ci daya mai ban haushi. Wannan ne nasara ta shida da Reds ta samu a wasanni bakwai, wanda ya ba ta damar shan gaban Manchester City wacce da jibin goshi ta samu rinjaye a kan Fulham da ci uku da biyu. Ita kuwa Arsenal tana ci gaba da kusantar City sakamakon nasarar da ta samu a kan Southampton da ci uku da daya, yayin da kuma Manchester United da Aston Villa suka tashi canjaras babu ci. A kasar Spaniya kuwa FC Barcelona ta sake farfadowa mako guda bayan da ta sha kashi a hannun Osasuna, inda a wannan karon ta samu nasara a kan Alaves da ci uku da nema. A yanzu dai Bercelona na gaban Real Madrid da maki uku, duk da doke Villarreal da ta yi da ci biyu da nema. Ita dai Madrid ta samu gudunmawar Kylian Mbappé da babban mai horaswar kasarsa Faransa, Didier Deschamps ya ki sanya shi a jerin sunayen da za su buga a wasannin kasa ka kasa.

Tennis | Coco Gauffs | US-Open
Shahararriyar 'yar wasan kwallon Tennis Coco GauffHoto: Charles Krupa/AP/picture alliance

'Yar wasan tennis ta Amurka Coco Gauff mai matsayi na shida a duniya, ta mamaye 'yar Jamhuriyar Cek Karolina Muchova mai matsayi na 49 da ci shida da daya da shida da uku a wasan karshe na gasar WTA 1000 ta birnin Beijing  a ranar Lahadi. Gauff da ta lashe gasar US Open ta 2023, ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen lashe gasarta ta biyu a bana bayan nasarar da ta samu a Auckland a watan Janairu. Tuni ma Ba'amurkiya Gauff ta samu fa'idar nasararta, inda ta haura zuwa matsayi na hudu yayin da Aryna Sabalenka ke a matsayi na biyu. Ita kuwa Iga Swiatek ta ci gaba da kasancewa lamba daya a duniya, a bangaren mata. Dama Carlos Alcaraz ya lashe kofin bangaren maza na gasar Beijing tun a ranar Laraba.