Wasanni: Gasar Olympics ta birnin Tokyo
July 26, 2021A Jumma'ar da ta gabata aka bude gasar wasannin Olympics ta bana a birnin Tokyo na kasar Japan. Bikin bude gasar ya samu halartar manyan baki kusan 1000 kawai, saboda annobar cutar coronavirus da duniya ta samu kanta a ciki. Wasannin suna gudana a yanayi na dokar ta baci da aka sanya karo na hudu a yankin Tokyo baki daya, saboda dakile yaduwar coronavirus din. Firaminista Yoshihide Suga na Japan yana da fata kan wasannin na Olympics ba tare da 'yan kallo ba su gudana cikin nasara, duk da yanayin da ake ciki na annobar. Kafin soma gudanar da shagulgulan bude taron da aka takaita, an yi tsit na minti guda domin nuna alhini ga miliyoyin mutane da suka rasa rayukansu sakamakon annobar coronavirus din a duniya.
Tuni dai aka fara lashe lambobi, inda Amirka ke kan gaba da lambobin zinare bakwai azurfa uku tagulla hudu jimilla 14. Yayin da Chaina ke matsayi na biyu da lambobin zinare shida azurfa uku da tagulla shida jimilla 15. A matsayi na uku akwai Japan mai masaukin baki wadda ke da lambobin zinare shida azurfa daya da tagulla biyu, baki daya tana da lambobi tara ke nan. Ita kuwa Jamus kawo yanzu ta samu lambobin tagulla guda uku, kuma tana matsayi na 36 tsakanin kasashen duniya. 'Yar wasan Taekwando daga Tekiath Ben Yessouf daga Jamhuriyar Nijar ta samu nasara a wasan farko. Daga nahiyar Afirka, kasar Tunisiya kadai zuwa yanzu ta samu lambar yabo ta zinare daya da azurfa daya.