Wasanni: Gwanaye a lig-lig din Turai
May 6, 2024A daidai lokacin da ya rage makonni hudu a kammala kakar wasanni a La Ligar ta Sipaniya, kungiyar ta birnin Madrid na gaban Girona da maki 13 a yanzu haka bayan da ta lallasa Cadiz da ci uku da nema. Duk da Girona ta lallasa abokiyar gaba FC Barcelona da ci hudu da biyu a makon na 34, hakan bai hana Real Madrid din samun damar zama zakara ba tare da kare bin damo ba saboda Girona ba za ta iya cike wannan gibi ba.
A Holland kuwa PSV Eindhoven ce ta zama zakaran da Allah ya nufa da cara a karo na 25 a wannan kakar wasanni da rikice-rikicen da ba a taba ganin irinsa ba suka mamaye ta, kuma suka girgiza abokiyar hamayyarta Ajax Amsterdam. Ita dai PSV Eindhoven ta tabbatar da kambunta ne bayan da ta yi nasara da ci hudu da biyu a kan Sparta Rotterdam. Da ma dai 'yan wasan da Peter Bosz ke horaswa wadanda suka sha kashi daya kacal a lig din Holland a bana, na bukatar maki daya ne kawai su lashe kambun. A daidai lokacin da ya rage makonni biyu kafin karshen kakar wasanni, PSV na da maki 87, inda ta zarta Feyenoord da ke a matsayi na biyu da maki tara.
A Portugal ma bakin alkalami ya bushe, domin kuwa Sporting Portugal ta lashe kambun zakaran kwallon kafar kasar a karo na 20 bayan da daya babbar kungiyar birnin Lisbon wato Benfica ta sha kashi a hannun Famalicao da ci biyu da nema a mako na 32. A daidai lokacion da ya rage makonni biyu a kawo karshen kakar wasa, Sporting ta yi nasara a gida a gaban Portimonense da ci uku da nema, lamarin da ya ba ta damar yi wa Benfica ratar maki takwas da ba za ta iya cikewa ba.
A Ingila duk da cewa da sauran rina a kaba game da zakara, amma Liverpool ta taka rawar gani bayan da ta caskara Tottenham da ci hudu da biyu a wasan da ke zama na kusa da na karshe da Bajamushen koci Jürgen Klopp ke halarta a Anfield. Wannan sakamakon dai, Aston Villa ta yi maraba da shi saboda duk da doke ta da Brighton ta yi da ci daya mai ban haushi tana sa ran jin kamshin cancantar shiga gasar zakarun Turai. Chelsea ta mamaye West Ham da ci biyar da nema, yayin da Totenham ta baras da wasanta na hudu a jere. A yanzu dai Arsenal ce ke kan gaba a Premier League da maki 83, yayin da Manchester City ke biye mata da maki 82 ita kuwa Liverpool ta kasance dutsen kafa murhu na uku da maki 78.
A fagen kwallon kafar Jamus kuwa, Bayer Leverkusen da ta riga ta zama zakara, ta ci gaba da cin karenta ba babbaka a wasannin mako na 32. Bayer Leverkusen ba ta yi wa Frankfurt da wasa ba, inda ta gyara mata zama da ci biyar da daya lamarin da ya sa zakaran ta kwalon kafar Jamus tsawaita tarihinta na gudnar da wasanni 48 a gida da waje a jere ba tare da ta baras da ko da daya ba duk da mai horas da 'yan wasan kungiyar Xabi Alonso ya sauya 'yan wasa takwas daga cikin 11 da suka doke As Roma da ci biyu da nema a wasan kusa da na karshe na Europa League. Baya ma da kwallaye biyun da suka zura wa Frankfurt kafin a tafu hutun rabin lokaci, 'yan wasan Leverkusen sun matsa kaimi inda suka ci kwallaye uku ciki har da wnda Boniface na Najeriya ya zura. Wanna ya sanya Alonso ya yi imanin cewa, akwai sauran kallo game da rawar da 'yan wasansa za su ci gaba da takawa a nan gaba.
Bayern Munich ta sha kashi tamkar kurar roko da ci uku da daya a filin wasa na Stuttgart, lamarin da ke zama farau a cikin shekaru shida. Rabon da Stuttgart ta doke Bayern Munich tun watan Mayun 2018, inda aka tashi hudu da daya. Ita kuwa Borussia Dortmund laya ta yi mata kyan rufi, inda ta doke Augsburg da ci biyar da daya. Godiya ta tabbata ga dan wasan da zai bar BVB a karshen wannan kakar bayan shafe shekaru 12, wato Marco Reus wanda ya zura kwallaye biyu. Ita kuwa Wolfsburg ta garin da ake kera motocin Volswagen ta mamaye Darmstadt da ci uku da nema, yayin da Bremen da Mönchengladbach suka tashi biyu da biyu kamar yadda RB Leipzig ta yi kunnen doki daya da daya da Hoffenheim.
A nahiyar Afirka, tsamin alakar da ke tsakanin Aljeriya da Maroko na mummunan tasiri a fagen tamaula, lamarin da ya sa hukumar kwallon kafa ta Afirka yanke hukunci mai tsauri. Kwamitin da ke kula da tsara gasanni na CAF ya yi zama a birnin Alkahira tare da yanke hukuncin bai wa kungiyar RS Berkane ta Maroko tikitin zuwa wasan karshe na neman lashe kofin CAF, bayan takaddama da ta fuskanta da US Algers kan taswirar yammacin Sahara da ke kan rigar 'yan Maroko. Sau biyu aka dage wannan wasan kusa da na karshe saboda rashin fahimta tsakanin kungiyoyin biyu, wadanda gwamnatinsu suka dade suna gaba kan yankin yammacin Sahara. Sai dai a yanzu Aljeriya da Maroko da suka yi fice a harkar tamaula a Afirka na barazanar fuskantar takunkumi daga CAF, idan suka ci gaba da shigar da rikicinsu na diflomasiyya a fannin kwallon kafa na kasa da kasa.
Dan Birtaniya Lando Norris ya yi abin kai a fagen tseren motoci, inda a karon farko na tarihinsa ya lashe gasar Formula 1 a birnin Miami na kasar Amurka. Babban abin sha'awar ma dai shi ne, yadda dan tseren na kungiyar Maclaren mai shekaru 24 ya kasance a sahun na shida amma kuma ya yi nasarar doke wanda ya zama zakaran duniya sau uku Max Verstappen na kungiyar Red Bull da kuma Charles Leclerc na tawagar Ferrari. Shi kuwa dan kasar Sipaniya Carlos Sainz na tawagar Ferrari ya samu matsayi na hudu, a gaban wanda ya zama zakaran duniya na Formula 1 sau bakwai wato dan Birtaniya Lewis Hamilton na tawagar Mercedes. Sai dai har yanzu Max Verstappen na ci gaba da zama zakaran duniya sakamakon lashe Grand Prix hudu daga cikin biyar da suka gudana a bana, lamarin da ya ba shi damar samun maki 136. Shi kuwa dan tseren kasar Mexico Sergio Perez yana biya masa baya da maki 101, yayin da Chales Leclerc na kasar Faransa ke a matsayi na uku a dunyia da maki 98.
Dan wasan kwallon tennis na kasar Rasha Andrey Rublev da ke a matsayi na takwas a duniya, ya lashe gasar Masters 1000 ta birnin Madrid a karshen mako ta hanyar hambarar da Félix Auger-Aliassime na Kanada a daidai lokacin da ya rage makonni uku kafin a fara gasar Roland-Garros. Wannan dai shi ne karo na biyu da Rublev mai shekaru 26 ya samu kambu a Masters 100, gasa ta biyu a daraja a fagen tennis bayan na Grand Slam. Yanzu dai Rublev ya haura matsayi na shida a duniya, wuri daya daga mafi kyawun matsayinsa wanda ya kai a watan Satumba 2021.