Ƙatar ta bude kofin duniya da kafar hagu
November 21, 2022Duk da kakkausar suka da caccakar da ta dinga sha daga kungiyoyi da kasashen duniya, daga karshe dai, kasar Ƙatar, ta gudanar da kasaitaccen bikin bude gasar cin kofin duniya ta 2022, bikin da ya dauki wani sabon salo mai ban mamaki.
A wasan farko kasar Ecuador daga yankin Latin Amirka ta doke mai masaukin baki Ƙatar da ci biyu da nema, inda kasar ta Katar ta zama ta farko a duniya da ta dauki nauyin gasar ta kuma gaza samun nasara a wasan farko.
A wannan Litinin aka fafata wasa na biyu na wasannin neman cin kofin kwallon kafa na duniyar a kasar ta Katar inda kasashen Ingila da Iran suke kece raini a rukuni na biyu na B.
Sauran kasashen da ke fafatawa a Litinin din nan sun hada da Senegal da ke yankin yammacin Afirka kuma daya daga cikin wakilan nahiyar Afirka biyar, za kuma ta fafata ne da kasar Netherlands.
Ita dai kasar Senegal za ta yi wasa ba tare da Sadio Mane ba shahararen dan wasan kasar da ya samu rauni gabanin fara wasannin na duniya. A cewar tsohon sakatare hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Najeriya, Sani Ahmed Toro haka zai iya tasiri ga bajintar da kasar za ta nuna.
A ranar Talata a rukunin C, Ajentina za ta kece raini da Saudiyya ita kuma Mexiko da Poland, inda a rukunin D, Denmark za ta kara da kasar Tunisiya, daya daga cikin wakilan Afirka a gasar, kana Ostraliya da Faransa. Faransa ke rike da kambun wasan bayan samun nasara a shekara ta 2018 lokacin da aka yi wasan a kasar Rasha.
'Yan wasan Poland dai sun samu rakiyar jiragen yaki guda biyu a kan hanyarsu ta zuwa kasar ta Katar domin halartar gasar. Hakan ta faru ne sakamakon yakin da ke faruwa bayan Rasha ta kaddamar da kutse kan kasar Ukraine, yayin da hukumar kula da wasan kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar da Rasha daga shiga wasannin saboda wannan yaki.