Labarin wasanni
June 13, 2018A ranar Alhamis 14 ga watan Yuni shekarar 2018 ake bude gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya karo na 21 a birnin Mosko. Shahararren filin wasan na Loujniki na birnin na Moscou ne zai karbi bikin bude wasan. Za a yi karawar farko ta bude wasan tsakanin mai masaukin baki Rasha da kuma Saudiyya a filin wasa na Loujniki na birnin Moscou. Washe gari 15 ga wata wakillan Afirka za su shigo fage inda Masar da ke a cikin rukunin A tare da kasashen Uruguay da Rasha da Saudiyya za ta kara da Urugay, kana Maroko da ke a rukunin B da kasashen Potugal da Spain da Iran ta yi karan kummallon wasan da Iran. Najeriya wacce ke a rukunin D da kasashen Kuroshiya da Island da kuma Ajentina za ta buga wasanta na farko a ranar Asabar 16 ga wata da kasar Koroshiya. Sauran wakillan na Afirka: Tunusiya da ke a rukunin G tare da Ingila da Begiyam da Panama za ta buga wasanta na farko da Ingila a ranar Litinin 18 ga wata a yayin da a rukunin H wanda ya kunshi Senegala da Poland da Japan da Kwalambiya, Senegal za ta yi bisimillar shiga wasan a ranar Talata 19 ga wata da kasar Poland.
Taurarin dan wasan kasar Masar Mohamed Salah wanda ya ji rauni a kashin bari wargi na allon kafada a gasar cin kofin zakarun Turai da Kungiyar Real Madrid bai halarci wasan motsa jiki na farko da kungiyarsa ta yi a jiya ba bayan isowarta a aksar ta Rasha. kuma likitansa Mohamed Abou al-Ela ya ce ya zuwa yanzu babu tabbas ko Salah zai samu damar shiga wasan farko da Masar din za ta fafata da kasar urugay a ranar 15 ga wata. domin a cewarsa har yanzu yana jin radadin raunin nasa wanda likitan ya ce ga al'ada na bukatar makonni uku kafin ya warke.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sanar da cewa akwai yiwuwar ta halarci gasar ta kasar Rasha a daidai lokacin da mahukuntan Birtaniya suka dauki matakin kaurace wa wasan a sakamakon badakalar bayar da guba da birtaniyar ke zargin Rasha ta yi ga wani tsohon jami'in leken asirinta da ke da zama a kasar ta Birtaniya. Angela Merkel ko da shi ke kasarta ta kori wasu jami'an diplomasiyyar Rasha kan wannan lamari, Jamus na raba batun siyasa da na wasanni. a dan haka za ta halarci gasar domin bai wa kungiyar Mantchaff kwarin gwiwa. Jamu wacce ke saman tebirin kwalon duniya na hukumar FIFA da kuma ke rike da kofin na duniya za ta yi kokarin kare kabbunta a wannan karo. A gasa 19 da ta shiga ta cin kofin duniya Jamus ta lashe gasar so hudu wato a 1954 da 1974, 1990 da kuma 2014. Ta baras da wasan karshe so hudu a shekara ta 1966 da 1982, 1986 da kuma 2002.
Ya zuwa yanzu dai kusan illahirin kungiyoyin kasashen 32 da za su fafata sun iso a masaukinsu a garuruwa daban-daban na kasar ta Rasha. Daga cikin wadannan kasashe 32 kasar Brazil daga Latin Amirka ne ke zamo daya dayar kasar da ba ta taba fashin halatar gasar ta cin kofin kwallon kafa na duniya a shekara ta 1930, inda ta halarci gasar sau 21. Jamus daga nahiyar Turai na bi mata a matsayin ta biyu da halarta 19. Ajentina daga nahiyar latin Amirka ita ce ta uku inda ta halarci gasar so 17. Daga bangaren wakillan nahiyar Afirka a wannan gasa ta bana, Najeriya na a sahun gaba inda za ta halarci gasar a karo na shida, Maroko da Tunnusiya wannan shi ne karo na biyar da kowacensu za ta halarci gasar, Masar ta je so uku Senegal so biyu.
A fannin yawan daukar kofin duniyar na kwallon kafa kuwa. Kasar brazil ce ke a sahun gaba da kofi 5, Jamus da italiya na bi mata kowane da kofi hurhudu. Ajentina da Urugay sun dauka so biyu-biyu a yayinda Faransa da ingila da Spain suka dauka so daya daya.
Daga lokacin soma gasar cin kofin kwallon kafar a shekara ta 1930 zuwa gasar karshe a shekara ta 2014 an zura kwallaye 2377, kuma Miroslav Klose na kasar Jamus shi ne dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya inda ya zura kwallaye 16, Ronaldo na Brazil na bi masa da kwallaye 15, Gerd Müller na Jamus na a matsayin na uku da kwallaye 14.
Kuma Roger Milla na kasar Kamaru shi ne dan wasan mafi yawancin shekaru da ya ci kwallon kafa bayan da yana dan shekaru 42 da wata daya ya ci kwallo a karawar da Kamaru ta yi da Rasha (6-1) a 1994.