Weah da Boakai za su fafata a zaben Laberiya
October 25, 2023Shugaban Laberiya George Weah wanda guda ne daga cikin ‘yan takara 20 da suka fafata a zaben kasar da aka yi a ranar 10 ga wannan wata na Oktoba dai na kan gaba a zagayen farko. To sai dai kuma shugaban na Laberiya bai samu kuri'un da za su ba shi galaba kai tsaye ba, saboda karantar rata da ke tsakaninsa da madugun adawa, Joseph Boakai wanda shi ne yake biye masa.
Karin Bayani: Fargaban faruwar tashin hankali a zaben Laberiya
Hakan na nufin za a je zagaye na biyu a zaben da ya kasance fafatawa irinta ta farko a tsakanin manyan masu takarar a zaben na Laberiya, kamar yadda hukumar zabe ta sanar. Inda shugabar hukumar zaben kasar ta Laberiya Davidetta Brown Lansanah ya ce sakamakon zaben ya nuna cewa babu dan takarar da ya samu kashin abin da ya dan zarta 50% kamar yadda ake bukata bisa doka, don haka ne ya sanya dole tafiya zagaye na biyu na zabe wanda za a yi a ranar Talata 14 ga watan gobe na Nuwamba. Kuma za a yi zabe ne a tsakanin wadanda suka fi samun rinjayen kuri'u, wato dai takara ce tsakanin dan takarar CDC George Manneh Weah da kuma dan takara na jam'iyyar Unity Party ko kuma UP da Joseph Nyumah Boakai ke jagoranta.
Hukumar zaben Laberiya dai ta ce an fito sosai a zaben na ranar 10 ga wannan wata na Oktoba, inda aka samu kashi 79% daga cikin adadin mutum miliyan biyu da dubu 400 da aka yi wa rajista.
Da kuri'u sama da kashi 60% ne dai Shugaba George Weah wanda tsohon zakaran kwallon kafa ne ya yi galaba a kan Joseph Boakai a zaben da aka yi a shekara ta 2017. Bangaren hamayya wato babbar jam'iyyar Unity Party dai ta ce tana tuntubar wasu karin jam'iyyu, domin yi wa jam'iyyar CDC taron dangi, a cewar wani Mohammad Ali na jam'iyyar ta adawa a Laberiya:
Bayanai sun tabbatar da cewa akwai jami'an zabe mutum tara da ke hannun ‘yan sanda a halin yanzu, bayan zarginsu da aka yi da saba dokar zabe a lokacin da ake lissafa kuri'u. Kasar ta Laberiya dai na cikin jerin kasashe matalauta a duniya, duk da kasancewar ta mai arzikin albarkatun karkashin kasa.
Kuma dama daga cikin ‘yan kasar na damuwa da munin da cin hanci da rashawa ke yi, sannan kuma har yanzu hankalinsu bai gama kwanciya ba, musamman a kan yakin basasar da suka gani a tsakanin shekarar 1989 zuwa 2003 inda sama da mutum dubu 250 suka salwanta. Kuma har yanzu ba kai ga hukunta wadanda ake zargi da haddasa shi ko ma wadanda suka aikata laifukan yakin ba.