Laberiya na zaben shugaban kasa
October 10, 2023Daga cikin 'yan takara wadanda ke fafatawa a zaben har da tsohon mataimakin shugaban kasar, Joseph Boakai da ke zama babban mai kalubalantar shugaba Weah. Manyan jami'iyyun siyasar kasar sun yi alkawarin gudanar da zaben cikin lumana a kasar da ke yammacin Afirka. Sai dai arangama tsakanin magoya bayan jami'iyyun kasar a baya-bayan nan na haifar da fargaba a zukanta jama'a.
Karin bayani: Fargaban faruwar tashin hankali a zaben Laberiya
Yaki da cin hanci da karbar rashawa na daga cikin alkawaru da 'yan takara suka yi idan suka lashe zabe, kasancewar laberiya na sahun gaba a kasashen da ke fama da wannan matsala a duniya. Tuni dai aka tura masu sanya ido kan zabe na kungiyoyin Tarayyar Turai EU da Tarayyar Afirka AU da na ECOWAS da kuma Amirka.