Laberiya na zaben 'yan majalisar dattawa
December 20, 2014Al'ummar kasa Laberiya sun fita kada kuri'arsu a yau Asabar dan zaben cike kujerun majalisar dattawan kasar, a wannan kasa da annobar Ebola ta daidaita.
Wannan zabe da za a cike kujerun 'yan majalisar dattawan 15 an dage shi har sau biyu bayan da annobar Ebola ta mamayi wannan kasa tare da hallaka mutane 3,290.
An dai fara zaben ne da misalin karfe bakwai da rabi a gogon GMT kuma za a kammala shi da misalin karfe biyar na yammaci.
Fitaccen dan wasannan George Weah da ya taka leda a Kulob din Chelsea da AC Milan kafin da ga bisani ya koma gida a shekarar 2003 da dan gidan shugaba Ellen Johnson Sirleaf da wato Robert Sirleaf an daga cikin 'yan takara 139 da suke neman kujeru a majalisar.
George Weah dan shekaru 48 ya gaza samun nasara bayan da ya fito a ka fafata da shi a takarar shugabancin kasar a shekarar 2005 inda suka fafata da shugaba Ellen Johnson Sirleaf.