Ladabtar da Iran game da shirinta na nukiliya
September 3, 2010ƙasar Japan ta ƙaƙabawa tawararta ta Iran wani sabon takunkumin karya tattalin arziki sakamakon ƙin dakatar da shirin inganta sinadarin Uranium da hukumomin Teheran suka yi. Wannan matakin ya tanaji dakatar da hulɗar dipolomasiya da na siyasa tsakanin Tokyo da manyan jami'ai 24 na gwamantin Ahmedinejad. Kana takunkumin zai bayar da damar katse hada-hadar cinikayya da masana'antu 88 na ƙasar Iran.
Hukumomin Tokyo sun nunar da cewa, sabon takunkumin biyeyya ne ga ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya da ya bukaci ƙasashen duniya su matsawa Iran ƙaimi domin ta wi watsi da shirinta na nukiliya. Wannan takunkumin na Japan, ya zo ne wata guda bayan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta azawa Iran takunkumin da ke zama na huɗu tun bayan da aka fara takun saka da ita game da shirinta na inganta Uranium.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala