1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Lafiya Jari

August 20, 2021

Shiri ne a kan matsalar rashin haihuwa. Wannan matsala ce da kan sanya ma'aurata neman mafita ta hanyoyi da dama. Shirin ya duba taimako da ake iya samu ta hanyar fasahar IVF da kwararru suka amince da shi.

https://p.dw.com/p/3zH8s

Ba da dadewa ba ne duniya ta yi bukin da aka kira ranar IVF na duniya. IVF harrufa ne da suka takaita abin da ake kira a turance Invitro fertilization, wato fasaha ce da ke taimaka wa wadanda suka dade suna neman haihuwa da kansu amma bas u samu ba, sai fasahar ta taimaka musu wajen samun juna biyun ta hanyar hada kwayoyin haihuwan na miji da na mace kafin a sanya shi a cikin mahaifa dan cikin ya kama. A Australiya a shekarar 1980 aka sami haihuwa na farko daga wannan fasahar bayan da aka yi ta gwadawa ana samun bari, kuma a yanzu haka ana hasashen a cikin kowane haihuwa 20, an yi amfani da fasahar a akalla haihuwa guda.