Lafiyar Iraki: Janyewar sojin Amurka...Iran
May 5, 2007An kammala taron kolin makomar kasar Iraqi a jiya cike da sabanin ra´ayoyi, daga jami´an diplomasiyyar da suka halarci taron.
A lokacin wannan tattaunawa, da aka gudanar a filin shakatawa na Sham- El Sheik dake Masar, Amurka tace ta gamsu da irin ci gaban da ake samu na kokarin tabbatar da zaman lafiya a kasar ta Iraqi.
To, Amma a waje daya , ministan harkokin wajen Iran, Manoucher Mottaki, kakkausar suka yayi ga matakan Amurka a kasar ta Iraqi, da cewa, ci gaba da kasancewar sojin ta a kasar shine ke haifar da yawaitar tashe tashen hankula da kuma rikice rikice.
Mahalarta taron dai na tsawon kwanaki biyu, sun yi alkawarin tallafawa kasar ta Iraqi da dalar Amurka biliyan 30 domin sake gina ta bayan yaki.
Har ila yau wakilan kasashen, sun kuma yi alkawarin yafewa kasar wani kaso daga cikin bashin da ake binta.