1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Laluben hanyoyin warware rikicin Gabas ta Tsakiya

August 9, 2013

Yahudawa da Palestinawa na shirin komawa teburin shawara bisa shiga tsakanin Amurika

https://p.dw.com/p/19NB5
File - President Barack Obama watches as Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu and Palestinian President Mahmoud Abbas shake hands, in this Sept. 22, 2009 file photo taken in New York. President Obama won the 2009 Nobel Peace Prize Friday Oct. 9, 2009 for "his extraordinary efforts to strengthen international diplomacy and cooperation between peoples," the Norwegian Nobel Committee said, citing his outreach to the Muslim world and attempts to curb nuclear proliferation. (AP Photo/Charles Dharapak, File)
Barack Obama,Benjamin Netanyahu da Mahmoud AbbasHoto: picture-alliance/AP

A mako mai zuwa za a koma teburin shawara tsakanin Isra'ila da Palestinu, bisa shiga tsakanin Amurika.

Jennifa Psaki kakakin ofishin Sakatariyar Harkokin wajen Amurika da ta bada labarin, ta yi karin haske:

ta ce:Za a koma Tattanawa tsakanin Isra'ila da Palestinu ranar 14 ga watan Ogusta a birnin Qudus, sannan kuma daga bisani a shirya wani taro a Jericho.Babban jikadan da Amurika ta wakilta a wannan tattanawa, Martin Indyk zai halarci taron.

Jennifa Psaki ta ce, za su amfani da wannan dama, domin dora duk matsalolin da ke hana ruwa gudu a kan tebur, da zumar samar da hanyoyin warware su.

Tun shekara 2010, aka watse baran-baran, tsakanin bangarorin biyu masu gaba da juna.

Sai karshen watan Yuli da ya gabata su ka sake ganawa a birnin Washington, bisa shiga tsakanin Sakataran Harkokin wajen Amurika John Kerry.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu