Awarding activists
February 5, 2014Tun a shekara ta 2004 ne dai Deutsche Welle ta kaddamar da wani shiri na saka wa masu fafutukar neman 'yanci ta shafunansu na yanar gizo da ake kira Blog. Inda tashar take bada lambar yabo ta Bobs tare da la'akari da wadanda ke rubuce-rubucen dake da nasaba da 'yancin fadin albarkacin baki, ba wai a kafofin yada labaru kawai ba, har da mutane a sassa daban daban na duniya.
"Kafin bayyanar wadannan hanyoyi na sadarwa, wadanda ke da damar samun kafofin yada labaru ne kawai ke da 'yancin fadin albarkacin bakinsu." Wannan su ne kalaman Jose Luis Orihuela, tsohon mamba a tawagar alkalan lambar yabo ta Bobs, kuma farfesa a harkokin sadarwa a jami'ar Navarra da ke Pamplona a kasar Spain.
Ya kara da cewar" tun bayan bayyanar shafunan yanar gizo na Blogs,'yancin fadin albarkacin baki ya kasance abun fafutukar karewa, kasancewar muryar mutum daya zai iya isa kowane bangaren duniya".
Wasan buya na Kenwa da Bera
Ya danganci inda mutum ya ke zaune, musayar ra'ayoyi tsakanin jama'a ya kasance wani abu ne da ke da hatsari, a daidai lokacin da 'yancin yanar gizo ya samu koma baya a sassa daban daban na duniya, sakamakon binciken kungiyar sa idanu kan 'yancin fadin albarkacin baki a shekara ta 2013.
" Muna ganin karuwar cin mutuncin da ake wa 'yan jarida da masu shafunan Blogs, wanda ya kamata duniya ta sa ido a kai," inji Hauke Gierow, shugaban sashin 'yancin fadin albarkacin baki a yanar gizo, na Kungiyar kare 'yancin 'yan Jarida ta kasa da kasa wato Reporters Without Borders, a nan Jamus.
Shekaru goma da suka gabata dai, ba boyayyen abu bane lura da harkokin da ke tafiya ta yanar gizo a kasashen China da Iran da wasu dake karkashin gwamatocin kama karya. Masu fafutuka da wadanda ke adawa da gwamnati, na da masaniyar cewar ana lura da lumaransu. Hakan ne yake sa suna yin taka tsantsan da rubuce-rubucensu tare da sakaye sunayensu don kada a tona asirinsu, wanda kai tsaye zai jefasu tarkon gwamnati.
Gwamnatin China ta dauki gagarumin mataki na kare jama'a daga samun hanyar shiga irin wadannan shafunan marubutan fafutukar neman 'yanci, wandanda take neman dakatarwa. An dai jima ana wasan buya na Kenwa da Bera tsakanin marubutan da mahukuntan. Wani binciken da Kungiyar kare hakkin 'yan Jarida ta kasa da kasa ta yi, ya nunar da cewar marubuta fafutukar 'yan ta yanar gizo kimanin 164 suke tsare a gidan kaso a sassa daban daban na duniya.
Bayan tonon sililin da tsohon jami'in hukumar leken asirin Amurka Edward Snowden ya yi, an gano cewar bawai al'ummar dake zaune a kasashen da ake mulkin kama karya ne suke da damuwa dangane da 'yancinsu ba. Takardun da Snowden ya bayyanar na tabbatar da cewar, hukumar leken asirin Amurka ta na satar bayanan hira ta wayoyi da gajeren sako tare da sakonnin Email da bayanan tarihin irin shafunan yanar gizo da mutane ke shiga.
Renata Avila da ke zama lauya mai fafutukar kare hakkin jama'a a Guatamela, kuma daya daga cikin Alkalan bada lambar yabo ta Bobs ta ce,
" tonon asirin da Snowden ya yi, zai taimaka mana wajen tuhumar wadanda ta hada baki da gwamnati suna leken asirin mutane, rage karfin tsarinmu tare rashin yarda da masu amfani da shafunan".
Rashin yarda
A yayin da mutane da dama a Amurka da wasu kasashen da ke karkashin mulkin demokradiyya suka yi imani tare da yarda da hukumomin gwamnati su kare su, daya daga cikin Alkalan Bobs Arash Abadpour ta bayyana cewar, tuni 'yan Iran suka dauki darasin kwana da sanin cewar, ya zamanto wajibi kowa ya lura da lamuransa.
Abadpour ta ce "abunda Snowden ya yi ya nunar da cewar, yarda wata aba ce ta tunanin mutane, domin wani lokaci na kan yi tunani dangane da ainihin manufar yarda".
Avila ta ce sai dai har an samar da irin wannan yarda ko aminta, mutane a sassa daban daban na duniya za su ci gaba da neman hanyoyin samar wa kansu kariya a yayin da suke musayar bayanai.
Karbar takardun shiga gasar Bobs
Tun daga ranar laraba(05.02.2014) ne dai, Bobs ke neman ra'ayoyin mutane akan muhimman ayyuka na karfafa gwiwa da yayata akidar goyon baya ga 'yancin fadin albarkacin baki da fafutuka ta yanar gizo. Masu anfani da hanyoyin sadarwa ta yanar gizo a sassan duniya na da tsawon wata guda na gabatar da takardunsu na shiga wannan gasa a cikin harsuna 14 ta wannan shafin www.thebobs.com